Mata Masu Jin Zafin Saduwa A Yayin Jima'i Ga Yadda Za Ku Magance Matsalar - Android Pols




A wannan karon ma dai cigaba ne akan darusan da nayi akan mata masu jin zafi idan ana jima'i wanda shima wannan kaɗai na iya hana ma'aurata jin daɗin zama aure,


A gaban mace akwai inda ake ƙira hymen akwai ta waje da ta ciki yana da tasiri wajen saduwar farko da mace za ta yi da namiji inda wannan na ciki ke fashewa yana fitar da wani ruwa kamar jini mace tana ganinsa ne lokacin da taje fitsari, a irin wannan yanayin mace na jin zafi sosai kafin wannan wajen ya warke shawara anan itace Mace tayi aiki da ruwan ɗumi sannan idan tanaso ta daina jin ciwon dole sai ana samun tazara a yin jima'i hakan shine zai saka a warke da wuri,


Har ila yau a gaban mace akwai wasu ƙuraje ƙanana da ido bai iya ganinsu sosai ana ƙiransu Cia cervix infection acne suna farawa daga farko har izuwa cervix hakan na faruwa idan mace ba ta magance ciwon sanyi ba kafin aure, ko kuma idan akayi rashin Sa'a mijinta yanada ciwon to idan maniyinsa ya taɓa wannan wajen sai ƙurajen su feso jajaye masu zafi ko ruwa mace ta zuba musu suna zafi ballantana saduwa, shawara shine, a irin wannan yanayin ki dage da shan maganin sanyi da wanda ake zama a ciki wato sitz bath. 


A kwai wani nau'in ciwon sanyi BVD bacterial vaginosis dryness wanda yake riƙe Ni'ima taki zuwa hakan yasa mace jin zafin jima'i, saduwa mace da namiji ba ta taɓa bada nishaɗi har sai an samu ni'ima irin wanda akeso wato ta zama fara kamar ruwa haka zalika yauƙi, shawara anan shine, irin wannan ki riƙe maganin sanyi me wanke dattin mara sannan maganin ni'ima sha yanzu magani yanzu kisha kafin jima'i, kiyi matsi da man ayu wanda kika haɗashi da man zaitun sannan wajen matsin kiyi amfani da sirinki.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post