Saƙonni sunyi yawa daga wajen mutane masu bibiyar mu musamman mata waɗanda suke fama da fitowar lankarwa a jikin su cewa suna buƙatar mu taimaka musu da magani akan yadda za su magnace wannan matsala. To bayan dogon bincike da mukai mun kawo muku wata hanya da za ku yi amfani da ita domin ku magance wannan matsalar ta lankarwa.
Yawancin mata idan suka haihu sukan samu jikin su duk lankarwa ta fito, wasu a cikin su zaka gani wasu kuma a cibiyoyin su wasu kuma duk jikin su. To ga dai maganin lankarwa a sauƙaƙe da za kuyi amfani dashi. Duk wacce take da lankarwa a jikinta kama daga ƙirjinta mazaunan ta cikin ta da sauran su kuma take so tayi maganin ta ga wani haɗi da za kiyi amfani dashi kiyi maganin ta gabaki ɗaya daga jikin ki.
Zaki samu gishiri kamar cokali biyu ki zuba a mazubi mai kyau, sannan sai ki samu khal-tupa wato venegar ki zuba kamar cokali 4 a cikin wannan gishirin da kika zuba a cikin mazubi sai ki juya shi sosai. sai ki samu auduga ki dinga dangwala kina gogawa a wajen da lankarwar ta fito miki. Idan kin gogawa za kiyi kamar minti 10 sai zuwa 20 sai ki samu tsumma da ruwan ɗumi kina shafawa a jikin naki.
To indai matsala ce akan lankarwa kodai a cinyarki ne ko cikin ki ko duk inda take fitowa to za'a samu sauƙi da waraka insha Allah idan za ki dinga yin wannan haɗin kina shafawa a duk inda take fito miki a jikin ki. Da fatan duk macen dake fuskantar wannan matsala za ta yi wannan. Sannan kuma idan kinsan ke baki da wannan matsala a jikin ki to ki sanarwa da sauran mata domin saƙon yaje wajen wanda suke da buƙatar sa.