Fitaccen Malamin addinin musulunci kuma babban limamin Masallacin juma'a na Dutsen Tanshi dake jihar Bauchi, Sheikh Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi, ya samu gurbi a gidan ajiya da gyaran hali, bisa zargin anfani da kalaman tunzura al'umma.
Lauyan Malamin mai suna Barista Umar Hassan, ya shaidawa manema labarai cewa, an gabatar da wanda yake karewa a gaban kotun majistare, bayan ya amsa gayyatar da jami'an yan sanda suka yi masa, wanda Alƙali bai samu beli ba, amma dai za'a sake zaman shari'a a ranar Talata.
A cikin watan Ramadan da al'ummar musulmi ke ibadar Azumi, Sheik Dutsen Tanshi ya bayyana cewa, baya neman taimako a wajen kowa, ko da Annabi Muhammad (S.A.W) ne, domin kuwa a wajen Allah kawai ake neman taimako, lamarin da ya haifar da kace-nace tsakanin al'ummar musulmi.