Kisan Kai: An Kama Matashin Da Ya Dabawa Mahaigiyarsa Wuka A Kano - Android Pols


A ranar Alhamis da musalin karfe 10 na dare, 'yan sanda a jihar Kano suka kama wannan yaro matashi dan shekara 22 mai suna Ibrahim da laifin caka wa mahaifiyarsa wuka ya kashe ta har Lahira. 


'Yan sandan Kano sunce da zaran sun kammala bincike za su kai yaron Kotu duk da ya riga ya amince shine ya kashe mahaifiyarta. 


Magabata dai suna cewa duk dan halal ko yatsa ba zai iya nuna wa iyayensa ba balle ya dakesu har ya kai ga kisa.


Mutane da yawa na ta bayyana ra'ayoyinsu akan lamarin inda wasu ke zargin watakila wannan yaron bai zo ta hanyar aure ba, ko kuma a gurin daukar cikinsa ba'a nemi tsarin Allah daga shaidan ba.


Shin yaya kuke kallon wannan al'amari? Ku bayyana mana ra'ayoyin ku akai. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post