Kira Zuwa Ga Iyaye Ku Ji Tsoron Allahu A Cikin Aurar Da 'Ƴa'yanku - Android Pols




Ya ku iyaye ku sani cewa: Baya halatta ku tilastawa 'ƴa'ƴanku auren wanda kukeso saboda ku kuke son shi amma su basa son shi.


Domin da yana halatta ayi hakan da Manzon Allah (S.A.W) bai bawa Barirah zaɓi akan mijinta ba. 


Hadisi cikin Bulugul Marami mai lamba 1036.

Ya ku iyaye ku sani cewa: Baku za ku zauna musu da waɗanda kuka tilasta musu aurensu ba, sune zasu rayu dasu, duk wulaƙancin da zai samesu, akansu zai ƙare.


Ya ku iyaye ku sani cewa: Allah da Manzon Allah (S.A.W) sun baku dama ku zaɓawa 'ƴa'ƴanku mazan aure nagari ko matar aure ta gari amma baya halatta ku tilasta musu, domin Manzon ALLAH (S.A.W) bai taɓa tilastawa wata ko wani hakanba.


Ya ku iyaye ku sani cewa: Da yawan 'ƴa'ƴanku da kukewa auren dole, da yawan mazan su kanyi amfani da wannan damar su wulaƙantasu, su kuma 'ƴa'ƴan naku ba za su iya kowa kukansu gareku ba, saboda ko sun zo da kukansu, ba za ku saurare suba.


Ya ku iyaye ina kira gareku kuji tsoron Allah akan 'ƴa'ƴanku ku aurar dasu ga waɗanda suke so kuma ku binciki halayen wanda suka gabatar muku, ku tabbatar da addininsa da ɗabi'unsa.


Ya ku iyaye kada abin duniya ya ruɗeku ku aurar da 'ƴa'yanku saboda kwaɗayi alhali ita ba ta sonshi, lallai Allah ta'alah yana cire albarka a cikin irin wannan aure.


Ya ku iyaye kuji tsoron Allah ku sani aure anayinsa ne domin neman yardar Allah, kada ku aurar da 'ƴa'ƴanku saboda masalaharku ta duniya.


Ya ku iyaye idan kuka aurar da 'ƴa'ƴanku ku rinƙa zama dasu lokaci-lokaci kuna bincikar halin da suke ciki ta hanyar ilimi da tsoron Allah kada ku karkata ɓangare ɗaya, kuma kada ku goyi bayan yaranku kuma kuyi adalci, kuma ku daidaita akan gaskiya a tsakaninsu.


Ya ku iyaye kuji tsoron Allah ku sani yanzu muna wani zamani wanda samari akwai ƙarancin aiki da ilimi, da kuma son duniya da son ƙyale-ƙyale, wasu mazan suna auren matane saboda kyansu, wasu kuwa suna aurene saboda wani abu mai ɗaukar hankali daga jikin mace.


Ya ku iyaye ku sani cewa: Da yawan maza da sun auri mace sun kusanceta na sati 1 ko 2 ko sama da haka to shikenan batada wata daraja a gurinsu, lallai wannan yana faruwa ga waɗanda sukayi auren soyayya ma, to inaga waɗanda aka yiwa auren dole.


Ya ku iyaye ku sani dukkaninku ababen tambayane a gaban Allah za'a tambayeku akan amanar da aka baku ta 'ƴa'ƴanku.


Ya ku iyaye ku daina biyewa son zuciyarku, ku daina bin al'adu, duk abinda zakuyi ku aunashi da Alƙur'ani da sunnah, kuma ku daidaitu akansu, 


Amma idan kuka kauce musu tabbas zaku sami matsaloli a cikin rayuwarku, wannan shiyasa iyaye dayawa ke fadawa cikin rashin lafiya da hawan jini da sauransu.


Ya ku iyaye ku tausayawa 'ƴa'ƴanku ku bisu a hankali, ku tabbatar da wanda zasu aura mutumin kirkine, domin kuwa akwai auren da gwara mace ta koma ga Allah bata taɓayin aure ba, da ta koma ga Allah tana mai aure amma kuma ta shiga wuta, saboda dalilin kasa sauke hakkokin aurenta, 


Duk kuma hakan yana faruwa ne saboda bata sonshi, rashin so kuma yana sawa mace ta kasa yin biyayya ga mijinta..


Ya ku iyaye ku sani tilastawa 'ƴa'yanku wajen aurar dasu ga wanda basa so yana iya jawo muku faɗawa cikin azabar Allah domin duk abinda yafaru na ɓarna a cikin zamansu kune sila.


Ya ku iyaye munaƙara kira gareku lallai aure ba abin wasa bane, kada kuyi hukunci a cikinsa da son rai, lallai Allah zai tambayeku akan yadda kuka aurar da 'ƴa'ƴanku.


Ya Allah ka bawa iyayenmu ikon sauke nauyin daka ɗora musu na 'ƴa'ƴansu. 


Ya Allah ka yafe musu kurarensu ka kuma azurtasu da aljannah.


Ya Allah ka azurta maza daga cikinmu da mata daga cikinmu da abokan zama nagari.


Ya Allah ka nesantamu daga zaluntar juna a cikin zamanta-kewarmu baki ɗayanmu.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post