Ga wasu jerin hanyoyi na hade-hade na Karin Ni'ima da sha'awa da mata za su yi amfani dasu
1 Hadin Kwakwa
kwakwa
dabino
madara ruwa.
Ki markada kwakwar da dabino sannan sai ki kawo madarar ruwa ki hada ki sha, ki gwada abin ba'a cewa komai a wannan hadin.
2. Sabon Hadi
lemon zaki
madara ta ruwa
zuma
Ki matse lemon sai ki kawo madara ruwa ki zuba zuma shima wannan hadin ki hada shi kiji yar'uwa
3. Hadin Gyada
wannan hadin yana sakawa ko wane lokaci maigida ya zama yana tare dake da farko zaki samu
gyada mai bawo
zuma
Ki samu gyadar ki sai ki hada ta waje daya bayan kin gyara sai ki markada sannan kuma sai ki tace ta daga nan sai ki kawo zuma ki zuba sai ki daukota ki saka a firji bayan wani lokaci ki daukota ki yini kina sha yar'uwa wannan hadin yana da ban mamaki sai kin hada kinji.
4. Ni'imar Diya Mace Itace Darajar Ta
Ki samu wannan abubuwan kamar haka :
Zuma
Habba Ta Gari
Man Zaitun
Za ki hada Zuma da garin habbatussauda mai kyau da man zaitun ki hade su wuri daya kina shan cokali biyu (2spm) da safe, cokali biyu da yamma har zuwa sati biyu (2wek).
Zaki ga yadda zaki rika tsiyaya lokacin saduwa in shaa Allah. Allah yasa sa mu dace
5. Saukar Da Ni'ima A Lokacin Jima'i
Ga wacce za ta iya shan danyen kwai to ki hadashi da madarar peak, ko danyar madarar rakumi ko ta shanu, ki gauraya sosai kisha sau uku kafin jima'i akalla awa uku kafin kwanciya(3hours before sex).
Da fatan mata za'a amfana daga wannan hanyoyin na samun Karin ni'ima a zamantakewar aure.