Idan nononki kananane kina so su yi manya kamar yadda kikeso dai-dai kina iya yin wannan hadin domin sanin lafiyar nonon Ki.
Ki samu
Cukwui
garin alkama
Aya
Nonon saniya ( ko madara ) Garin hulba ( ko man ).
Cukwui Wanda yawansa zai Kai guda uku sai Ki samu garin alkama gwangwani daya, sai Aya itama gwangwani daya, sai ki dakasu za su zama gari sai ki tankade.
Ki samu nonon saniya idan kuma bakya sha ki samu madara ki zuba wannan garin kamar cokali 3 Ki dama kina sha kullum sau 1 sannan ki lura lokacin da za ki yi wanka.
Ki tafasa ruwa da garin hulba a ciki ki bari yayi sanyi, sai ki wanke nonon da shi, sannan kiyi wankan, wannan hadin matar aure wacce tayi yaye za ta yi sannan budurwa za ta yi.