Wani dattijo da yai kusan shekaru 100 a duniya ya angawance da wata Matashiyar yarinya mai kimanin shekaru 14 cikin garin Abuja cewar wani, Hussaini Duma Jagaba.
Sai dai angon ya ce shi da sabuwar amaryar sa suna son junansu.
“Kamar yadda na shaida wannan auren ina addu’ar Allah ya kiyaye auren ya bamu zaman lafiya, cewar ango.
Amaryar dai mai shekara 14 da angonta mai shekara 95 sun Angwance ne a ranar Asabar din da ta gabata. A hirar da aka yi da dattijon bayan an daura auren, ya ce duk abin da mutane suka ce bai damu da hakan ba domin suna son junansu shi da amaryarsa.
Wasu suna ganin an tilasta mata ta aure ni saboda kudi, mutane su daina irin wannan tunanin domin tunani ne mara kyau,” Inji ango.
Kalli hotunan ;