Hilda Baci Bassey Yar Najeriya Sarauniyar Dafa Abinci Ta Duniya - Android Pols




Hilda Baci Bassey Yar Najeriya ta doke tarihin Kundin Guiness na duniya na tseren dafa abinci mafi dadewa a duniya.


Tata Tondon ‘yar kasar Indiya ce take rike da kambun bayan da ta shafe sa’o’i 87 da mintuna 45 a shekarar 2019 tana girki.


Sunanta na gaskiya, Hilda Bassey Effiong, matashiya ce mai dafa abinci a Nijeriya daga Karamar Hukumar Nsit Ubium ta jihar Akwa Ibom, Tana da wurin dafa abinci a Legas mai suna “My Food by Hilda” Cikin sharudan gasar dole ta tsaya ta yi girki na tsawon lokaci a tsaye ba tare da ta zauna yayin girkin ba.


Ba a yarda ta sha kofi ko abubuwan kara kuzari, ko wani abin sha don kara karfin jikin yayin dafa abinci. Zata yi girki na tsawon kwanaki 4 ba tsayawa. Ana yin gasar girkin ne a wurin shakatawa na ‘Amore Gardens’ da ke Lekki, Jihar Legas, Nijeriya.


Tana yin girki safe da dare da rana na tsawon darare 4 ba tare da yin barci ba.


Tana da hutun mintuna 5 kacal a kowace awa (ma’ana kowane awa 1, tana da hakkin ta huta na mintuna 5 kacal, wato hutun sa’a a kowane awa 12) An ba ta damar cin abinci, shan ruwa ko ruwan ‘ya’yan itace, da shan glucose.


Wasu majiyoyi sun ce Tana samun hutun mintuna 30 duk bayan sa’o’i 6, tana kwashe mintuna 30 a cikin motar asibiti da ke kusa da ita, inda za ta iya yin barci, ta yi amfani da dakin wanka, sannan ta sami tantancewar likita ko duba lafiyar ta daga tawagar likitoci.


Duk abin da ta dafa tana raba wa mutanen da ke wurin kyauta ba tare da sayar da abincin ba.


Takan dafa abinci daban-daban lokaci guda. Tana da ‘yancin dafa duk abincin da take so. Babu takurawa kan girkin da ta iya da wanda ba ta iya ba. Taken shiga gasar ta duniya shi ne ‘Dafa abinci cikin ƙayyadadjen lokaci’.


Kowane abinci da aka dafa da kowane farantin da aka ba da shi ana rubuta shi. Ta dafa abinci sama da kala 115 kawo yanzu.


Ta fara girkin ne a ranar Alhamis ta kammala Ranar Litinin 15 ga Mayu, 2023 da yamma.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post