A Rana Mai Kamar Ta Yau 15 Ga Watan Mayu 1976 A Ka Harbe Kanar Buka Suka Dimka.
Buka Suka Dimka.
Laftanar Kanar Buka Suka Dimka sojan Najeriya ne wanda ya taka rawa a juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar 13 ga Fabrairun 1976, Wanda Aka Kashe Shugaban kasar Nijeriya Janar Murtala Ramat Muhammad.
An kashe Laftanar Kanar Dimka a bainar jama'a a ranar 15 ga watan Mayu, shekarar alif 1976 a gidan kurkukun tsaro mafi tsaro na Kirikiri da ke Legas.
Laftanar Kanar Buka Suka Dimka ya kasance jigo a juyin mulkin da bai yi nasara ba a shekarar 1976 inda aka kashe shugaban kasar Najeriya Janar Murtala Muhammed. Da ya gane cewa juyin mulkin bai yi nasara ba, sai ya gudu zuwa Afikpo da ke Jihar Anambra a lokacin, ya nemi mafaka tare da wata tsohuwar budurwarsa.
Nan take bayan kashe Murtala, sai ya garzaya zuwa gidan radiyon Najeriya NBC domin bayyana nasarar juyin mulkin wanda bai sani ba har yanzu bai yi nasara ba. An kama shi ne a watan Maris, 1976. A watan Mayun 1976 Dimka da wasu masu yunkurin juyin mulki shida aka kashe su a bainar jama’a ta hanyar harbi da bindiga a gidan yari da ke Legas.