Hakika matsalar Istimna'i (wato Masturbation) da hausa ake kira da Zinar Hannu (kokuma duk wata hanya ta fitar da maniyyi ba ta jima'i ba, kuma ba a mafarki ba ) gagarumar matsala ce wacce take shiga zuciyar masu yinta, tayi KaKa-Gida.
Kuma ita wannan dabi'a idan mutane na yinta tana da wahalar fita gaba dayanta dole sai dai albarkacin addu'a da kuma yawaita ibada mutum zai samu wadatuwar tsoron Allah a zuciyarsa harma ya zamto ba zai iya aikatawa ba.
Na tattauna da mutane sama da dari biyu (200) a wannan satin yawanci suna kukan yaya za su yi su rabu da wannan matsalar su daina yi, suna cewa koda sun daina suna kara komawa basa iya bari. Wasu daga cikinsu suna cewa gaba daya basa iya haddace karatu a dalilin matsalar aikata Istimna'i ta kawo musu.
Wasu Kuma suna cewa haka kawai suke zubar da maziyyi koda wa'azi sukaji anayi akan mace, wasu kuma na cewa kankantar gabane yake damunsu, Wasu Kuma Ya haifar musu da matsalar ido, Wasu Kuma tsananin ciwon baya, Dan Allah ai ya kamata ko dan wannan illolin mutum ya tuba yabar aikata wannan dabi'ar.
Mafiya yawan samari suna yi ne bisa niyyar wai zasu kauce daga ZINA. Basu san cewa shima wannan din babban Kaba'ira bane.
Matasa Maza da Mata da dama sun afka cikin wannan bala'in. Wasu cikin rashin sanin illolinsa, wasu kuma saboda tsabar Fajirci.
Kuma kamar yadda zina take da mutukar Illa tana cutar da lafiyar mutum, ta cutar da hankalinsu, da gurbata tunaninsa, ta cire masa Kwayar Imani da tsoron Allah daga zuciyarsa.
To hakanan shima Istimna'i yake lalata rayuwar mutum da mutuncinsa da lafiyarsa. Lallai wajibi ne ga duk mutumin da yake son kansa da arziki, kuma yake fatan gamuwa da Allah lafiya, ya nisanci Zina da dangoginta irin su Luwadi, Madigo, Istimna'i, da sauransu. Kamar yadda ake ta fada anan a kafafen Wa'azantarwa da fadakarwa. Babbar hanyar da zaka bi/zaki bi domin rabuwa da wannan bala'i sun hada da;
1 Yin aure
2 Yawaita azumi
3 Nisantar duk wani hoto ko Video mai nuna tsaraici. (Ka gogeshi daga wayarka)
4 Nisantar shafukan Internet masu nuna tsaraici.
5 Daina abota da fitsararrun abokai / kawaye.
6 Nisantar duk wajen da ake chudanya tsakanin maza da mata.
7 Ka daina zama kai kadai a cikin daki in dai ba ibada kake yi ba.
8 Yawaita karatun Alkur'ani da zikirin Allah da sauran ayyukan alkhairi.
9 Zama cikin Mutanen kirki, karanta labaran mutanen kirki tare da kokarin koyi dasu.
10 Tuna Allah a ko yaushe da kuma tunowa kusancinsa gareka aduk inda kake.
11 Tuna kusancin ajalinka, fitar ranka, kwanciyar kabarinka, hisabinka, da kuma masaukinka na karshe. Wuta ko Aljannah.
12 Fita daga duk wani Group ko shafi na batsa a Facebook ko Whatsapp wanda suke kunshe da abubuwan batsa, tare da nisantar abokai masu sharing din abubuwa irin wannan.