An haifi Halima Aliko Dangote ( a kwaryar birnin Kano a Nigeria) 'yar kasuwa ce 'yar Najeriya, mai bayar da agaji wa mutane da dama,
Haka zalika Ita ce Babban Darakta na Gidauniyar Aliko Dangote da Dangote Industries Limited. Tana kuma aiki a hukumar Dangote Group.
Malama Halima Aliko-Dangote a halin yanzu ita ce babbar Darakta mai kula da harkokin kasuwanci a rukunin masana’antu na Dangote Industries Limited, inda take da alhakin gudanar da ayyukan raya kasa da aiwatar da ayyukan Dangote.