Kudi, mulki, daukaka dukkaninsu Allah ne yake baiwa duk wanda yaga dama, namiji ko mace, karami ko babba Mai addini ko mara shi.
Don haka mata suna cikin jerin mutanen da Allah Yake zaba ya musu dukiya, arziki ko kuma ya daukaka su. Sai dai koma wani irin matsayi mace take ciki babu abunda take bukata irin ta samu mijin da za ta aura. A hakan ne wasu mazan da basu da guda daga cikin wadannan abubuwan suke dace su auri irin wadannan matan.
Sai dai rashin sanin yadda za su zauna dasu yasa auren baya jimawa yake lalacewa. Idan kuma ya jima sai aga mijin nata ya dawo tamkar yaron gidanta.
Abokina idan kana auren Irin wadannan matan ko kana da niyyar aurensu, ga wasu dabarun yadda ake zama dasu kamar haka.
1: Idan kana son zaman aure na gaskiya da macen da ta fika samu. Ka zama mai gaskiya a duk halin da ka samu kanka. Kada ka sake ka rika yi mata karya ko ka ci mata amana akan wani abun da ta saka a karkashin kulawarka.
2: Kada ka sake ka barmata ragamar gidan a hannunta. Kada kace tunda ta fika kudi itace za ta rika yin komai. Ka daure ka yi hidimar gidan daidai karfinka idan taga dama ita ta kara da nata. Kada ka kauda kai wajen biyan irinsu kudin wuta, ruwa makaranta yaranka idan kun haihu sai idan itace ta kaisu makaranta mai tsadar da zata rika biya.
3: Kada ka sake kace kai bazaka yi wani abun ba saboda kana auren mace mai kudi ko mai matsayi. Ka nemi abun yi ko yaya yake kaima kana fita tana ganinka kana zuwa nema kamar yadda kowani magidanci yake yi.
4: Kada ka bari ta zama itace mai sawa ayi. Itace take da ikon fada. Itace ke bada umarni. Yi kokarin nuna mata kaine shugaban gidanka kuma dole a saurareka a kuma bi umurninka idan ana son zama lafiya.
Taka mata burki akan wani abunda take yi ko tayi ba dai-dai ba. Zama da irin wadannan matan dole ka kasance kashi 60 kai mai zafi ne kashi 40 ne ake iya samun kanka idan akayi sa'a yadda za ta rika samun shakku a ranta na gudun bata maka rai.
Ka kafa wasu dokokin da zaka nuna dole a bisu muddin kai ne mijin amma ba ka bari itace za ta maka hakan ba.
5: Kada ka sake ka zama ragon maza wajen Jima'i. Ka tabbatar da cewa a duk lokacin da ka daura mata sirdi baka saukewa har ta tabbatar da gamsuwarta da jin dadin ta. Kada ka bari sai idan itace take so za ayi.
Haka kawai ka rika takurata akan kana bukatar ta koda kuwa ba hakan bane domin kwance yin hakan daga gareta.
Muddin zaka zama jarumi a Jima'ince ga macen da ta fika kudi. To za a zauna lafiya idan ka hada da sauran shawaran baya.
Maza dayawa ba komai yake jawo musu raini da kaskanci ba wajen irin wadannan matan sai yadda suka kasance masu kwadayi da nuna musu abun hannunsu suke so.
Muddin mace mai kudi ko daukaka za ta fahimci kai ita kake so kuma da gaske, zaka moreta fiye da kowa a duniya. Amma da zaran ta fahimci kudinta ne a gabanka, ko ruwa ka bata sai tayi shakkun sha.