Jami'an tsaron farin kaya na DSS a Kano sun cafke matashin nan Baffa Hotoro da ake zargi da yin sakin baki ga Manzon tsira (s.a.w)
A watan azumin da ya gabata ne Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya sanar da cewa an kama matashin amma daga bisani Baffan ya fito a bidiyo ya musanta cewa an kama shi.
Amma a Alhamis ɗin nan hukumar DSS a Kano ta tabbatar wa da Freedom Radio cewa suna tsare da Baffa Hotoron.
Tags:
Labaran Duniya