Don Mata: Yadda Zaki Bambance Ruwan Dake Fitowa Daga Gabanki Na Cuta Ko Na Lafiya - Android Pols




Wani abu wanda da yawa mata basu iya rarrabewa shine bambamcin ruwan dake fitowa daga gabansu. 


Akwai ruwa kusan kala hudu dake fitowa daga gaban kowace Mace da zarar ta balaga. 

Wadannan ruwa kuwa sune kamar haka:-

1- Ruwan Ni'ima

2- Ruwan Maziyyi

3- Ruwan Infection

4- Ruwan Maniyyi

5- Akwai kuma ruwan kololuwar dadi(squard)


1- Ruwan Ni'ima:- shi wannan kusan kowacce Mace indai lafiyarta kalau kuma ta balaga ta san shi kuma shine ruwa mafi amfani a jikin Mace, domin yana bawa gaban mace kariya tare da yaki da kananun bacteria da ka iya cutar da gaban mace ko ma duka ilahirin gabanta. 


Domin ba a son gaban mace ya kasance a bushe kamar tayil. Yadda ruwan yake kuwa fari ne mai kama da normal ruwa, kuma "baya yauki" Sannan yana da kamshi, kamshin kuma ya ta'allaka daga abinda macen ta ci. Wani lokacin yana da dandanon kamar na ruwan tuffa ko roman.


Kuma yana zama a gaban Mace ko da yaushe in dai lafiyarta kalau. Shi yasa mutukar gabanki na bushewa to tun wuri ki nemi magani. 


2- Ruwan Maziyyi:- shi kuma wanna ruwa ne dake fitowa daga gabance a yayin da taji sha'awa. Kuma yana da yauki sosai sannan kuma fari ne shima kamar normal ruwa. 


Sai dai shi idan ya bushe yana dan yin zarni-zarni amma ba mai tashi ba. kuma yana da dandanon gishiri. Kuma ba'a wanka in ya fito kawai wankewa ake.


3- Ruwan Infection :-  shegen kenan shi wannan ruwa ne mai kauri kamar majina ko tsinkakken station, sannan yana da karni. Wani lokacin kuma yana kama da rubabbiyar madara, ma'ana yayi lite yellow. 


4- Ruwan Maniyyi:- wannan kowa ai ya san shi baku bukatar wani bayani, Illa dai ku sani mace bata fitar da maniyyi irin na namiji illa kawai sai dai taji kololuwar dadi. 


5- Ruwan Squad:- wannan ba kowace Mace take dashi ba, domin a cikin mata dubu ba'a samun daya da take dashi. Kuma yana zubowa Mace ne kawai yayin gudanar da jima'i. Baya wari baya karni kuma baya tsami. Sannan yana zubowa kamar fitsari.


Da fatan wannan darasin ya gamsar kuma ya amfanar. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post