Yana daga cikin abinda yake sawa mace ta rasa kima da mutunci, ta kuma zama wulaƙantacciya a gidan miji, Wato roƙon saurayinta tun kafin suyi aure, mace ta rinƙa tambayar saurayinta katin waya, ko kuɗin ankon biki, ko ta rinƙa saka shi yana yi mata siye-siye marasa ma'ana.
Tun daganan kimarta take ɓarewa a idonsa hardama kimar iyayenta, domin wasu iyaye suna bada gudun-mawarsu wa 'ƴa'ƴansu wajen roƙon Samari. Indai kika kame daga roƙon saurayi to babu wani saurayi da ya isa yazo miki da maganar banza a cikin soyayya ko ya yi miki kallon raini.
'Yan mata kuyi haƙuri da iya abinda Allah yabaku, lallai saurayi ba zai iya magance miki matsalolinkiba, Allah ne yabawa wannan saurayin abinda kike roƙonsa, kema kinema a gurin Allah domin dukkanku bayinsa ne.
Samari kuji tsoron Allah ku rinƙa kyautatawa 'ƴan mata a yayin da kuke soyayya dasu, ku rinƙa yi musu kyautuka domin ita kyauta tana ƙara danƙon ƙauna.
Sannan duk wanda ya lalata 'ƴar wani ko ƙanwar wani ko yayar wani da kuɗi mai yawa, to kaima za'aiwa ƙanwarka ko yayarka ko 'ƴar cikinka a kyauta, wannan haka yake.
Ya Allah yakawomana dauki maza da Mata samari da zawarawa yakawo qarshen zaman gida lafiya cikin aminci yabawa kowa masoyinsa na gaskiya mai addini yarabamu da bashi da kunci da damuwa duniya da lahira
Allah ka gafarta mana laifinmu kuskure da ganganchi yatsare gaba Ameen.