Zamani yai sauyin da a yanzu mata basa son haila ta samesu a cikin watan Ramadan da yawa saboda suna ganin yana yi musu wahalar ramawa bayan sallah, wanda hakan ke jawo su zaɓi shan magani domin dakatar da jinin.
Kamar yadda malamai suka tafi baki ɗaya sun gamsu akan babu haramcin yin hakan matuƙar likita ya tabbatar babu wani illa (side effect) da zai biyo baya nan gaba.
Anan akwai wani kuskure da Matan ke suke yi. "kunji Malamai cewa sukai muddin likita ya tabbatar komai lafiya" ba wai kurum don kinsha bakiji komi na matsala ba. Don haka kunga kenan shan maganin tsayar da haila daka ko don kawarki ta baki shawara kurum ba bisa umarnin likita ba tohfa wancan hukuncin bai shafe ki ba, cikar sharadin shine ki bi umarnin zuwa ki tattauna da likita ya binkici yiwuwar samun matsala ko rashin ta.
Duk wacce bata cika ka'ida ba taje tasha maganin daka tohfa yunwar banza tasha koda hailar bata zo ba, domin ke ba likita bace, don haka ya dace Mata ku yi hankali da wannan, Ba'a yiwa addini hawan ƙawara.
Musamman wasu hailar kan kamasu a farkon wata kaga kenan akalla tai kwana 20 zuwa 26 wata na shan magani kullum. Saɓanin wacce in a karshen Ramadan din hailar ke zuwa da baifi tasha na kwana 10 ba, domin maganin ana fara shansa ne tun kafin kwanakin da ake tsammanin hailar su cika da kwana 3 ko 4, har zuwa ranar da azumin zai kare.
Toh kunga ai akwai ban tsoro ace mutum nata kwasar hormonal pills alhalin yana Azumin da bana yini guda bane kadai ballantana. Wannan tasa akace a tuntuɓi likita: domin wani maganin hatsarin sa shine STROKES can gaba a rayuwa ba wai yanzu da ake jin komi normal ba, wani kuma in me estrogen ne hatsarin cancer can gaba ake gudu. Amma idan likita ya bincika profile dinki yaga ke ba'a tsammanin waccan matsalar daga gareki shikenan.
Shiyasa ba hujja bane don kawarki nasha kema kisha, Sam babu mutum biyu cikin halittar Allah Masu komi iri guda. Magani da yadda yake aiki jikin kowa.
Shyasa a ni dai banga dabara ba cikin fara shan pills musamman ga wacce haila ke zuwa mata farkon wata koda babu illah, domin idan kikai hakuri haila kwana 2 zuwa 5 ne galibi angama, yafi ai kwana 20 ko fiye ana hambuɗar kwaya! Koda lafiya ballantana hormonal ba a yabonsu kai tsaye koda anyi taka tsantsan.
Kukaga de duk abu irin na magungunan hana daukar ciki amma basa hana haila, ai kasan babbar abace. Datti ce.
Amma de kamar yadda na faɗa inhar likita kwararre ya tabbatar Mace bata da wani abin damuwa daka iya jawo illah nan gaba musamman a mata masu irin ciwon kai na Migraine ko wata cuta da bata haduwa da Maganin, yadda baza a cutu ba, shikenan a ya HALASTA. Amma fa likitan ya zamto ƙwararre ne yasan magani, aikinsa ne.
Hakazalik karmu manta waccan fatawar a duniyance kurum aka bada ita, amma kuma wajibi ne ɗan Adam ya duba al'amarin lahira
A Ɓangaren LAHIRA kwai abin dubawa.
Ita ibadah ako yaushe so ake kayi ta kana me sha'awa, walwala tare da jin daɗinta, bawai ka rika yi mata ci da karfi ba, wato ya zamto tsoronka bakaso kazo kana ramuwa bayan azumi. Wanda yake azumi saboda Allah babu ruwansa da wannan.
Koda nake likita nide a ko da yaushe in abu irin wannan yai CLASHING ga Addini ga kuma Kimiyya..... Toh nafi sha'awar naga mutum yayi abinda Allah da Manzonsa za su yi farin ciki fiye da fifita bukatar ransa.
Domin duk addu'oin da mutum zai yi koda yana haila za'a amsa masa, babu bambanci da addu'ar me haila cikin Ramadan ko mara haila, kurum Azmin ne da baki ba.
Azumin nan kuwa in muka duba tun zamanin annabi (AS) haka Mata ke yinsa, in haila ta zo su Dakata, Sannan daga baya su rama bayan ramadan.
Azumi fa Allah kadai yasan ladan me yinsa! Amma kukaga duk girmansa Allah yace a bari saboda haila, wanda yana daga cikin ginshiƙan dake riƙe da Musulunci yafa dace mutum yai aiki da hankali. Common sense.
Sannan duk girma irin na sallah wacce ko a filin yaƙi Allah bai yafewa mujahidai ita ba sai sun yi koda ana ɓarin wuta, kuma ko a ciwon ajali inde hankali bai gushe ba Allah yace nan ma bai yafe ba.
Kai karshen zancen cewa akai duk wanda yabar sallah guda ɗaya tak da gangan toh yayi ridda, ya rusa imani da musuluncin sa.
Amma duk da irin wannan horo da yin sallar. Allah yace lallai Mace kar tayi in tana haila, kuma ko bayan haila ba sai ta rama ba ya yafe mata. Ai inkika kalli wannan maganar ba ƙarama bace, Alama ce ta Allah na ganin girman haila.
Shiyasa akwai hadisi ingantacce da Annabi Muhammad (SAW) yace koda Mace tasha azumi dalilin haila duk randa za ta rama toh ladan Ramadan ɗin ne dai za'a bata, bai rageta da komi ba.
Annabi (SAW) yaje gidan Ummu Aɗi'ah a lokacin ana Azumi sai yake faɗawa Mata a lokacin cewa; idan ana azumi aka sami wasu waɗanda basa azumi sun zo suna cin abinci a gaban wanda ke ramuwar azumin toh ubangiji zai sa Malaiku su dinga yiwa mutum salati har sai lokacin dame cin abincin nan gaban me ramuwar Azumi zai gama.
Kunga Mala'ikun Allah kuwa ko guda 1 tak ne yai ma salati ai zance ya qare, Ka haye.
Domin cikin mala'iku akwai wanda bakunansa sun kai dubu saba'in,Sau 1 tak inya buɗe baki yaima salati ya kake tunani? Ballantana akwai wanda Allah kaɗai yasan adadin bakunansu.
Toh kunga inde Mace tasan akwai wannan don ta zo tana rama Azumi ai ba faɗuwa bace riba take samu. Domin sanda tabar azumin cikin Ramadan biyayyar Allah ce kuma ibada ce domin tabi umarnin Allah, sanda take ramawa ma ibadah take, sanda ake cin abinci gabanta ibada take.
Shiyasa Mata sun fi Maza tarin hanyoyin samun aljanna.
Da wannan sahabbai cikin Maza da Mata suka tsere mana, saboda suna ibadar ne tare da sha'awa da walwala, basa jin da kyar suke, ko tunanin abinda zai biyo baya yayin ramuwa. Sun-san Allah ba zai ragesu da komi ba, domin da Azmin da hailar duk shi akema.
Amma dai muddin lafiya aka tabbatar Mace take, toh shan Maganin ba haramun bane. Wallahu a'alam