Kukan jarirai da dare na daya daga cikin manyan abubuwan da ke takura iyaye, ya hana su sukuni da baccin dare, musamman ma idan haihuwar farko ce.
Wasu jariran ba sa barin mahaifiyarsu bacci da dare, sai dai su tsaya haka farke tsawon dare su na rainon jariri ta hanyoyin daban-daban domin samun ya yi bacci.
Hakan ya kan sa iyaye damuwa da tunanin menene dalilin da ya sa jaririn ke kuka, shin ko wani abu yake bukata ne? Abin mamaki ga iyaye shi ne, baccin jariri a rana amman kuma da dare yai ta fama da kuka.
Hajiya Fatima Umar, wata yar kasuwa mazauniyar Abuja, ta bayyana cewa tunaninta a duk lokacin da take da juna-biyu, damuwarta shi ne kukan daren jariri, saboda irin abinda ta fuskanta daga 'yayanta biyu lokacin da su ke jarirai.
“Wani lokaci sai na fara tunanin ko dai jaririna na ganin wani abu ne da ni bana gani wanda hakan ke sa shi kuka?,”in ji ta
Ta ci gaba da cewa, “a haihuwata ta biyu, sai da na dauki jaririn zuwa wurin malami domin yi masa adduá, saboda abin ya fara ban mamaki kullum zai fara kuka misalin 2 na dare sai kuma ya daina zuwa 5 na asuba.”
“To sai dai, makwafciyata ta ce min zai daina kukan zuwa wani lokaci, shikenan sai na hakura. Yana kai wata uku da haihuwa, sai kuwa ya daina kukan.”
Hajiyar, wacce ta ce ta kasa gane dalilin kukan jarirai, ta ce da sun kara girma kadan zuwa uku, shikenan sai kuma su daina kukan.
To amman, menene yake sa su kuka wanda kuma bashi da magani, ta tambaya?
Madam Amaka Njoku, wata ma'aikaciyar gwamnati a Abuja mahaifiyar yara biyar ta ce, dukkan yaran da ta haifa sun yi kukan dare, ta ce ta ma saba da rashin baccin dare a lokacin da take rainon su.
Amaka ta labarta cewa, lokacin haihuwar ta ta farko, akwai lokacin da ta dauki jaririn zuwa asibiti domin ganin kukan ya yi yawa sai take tunanin ko wani ciwo ne.
Amman, da likita ya duba, sai ya ce jaririn bai da kowace matsala a jikinsa.
Duk lokacin da na labarta wa abokanaina halin kukan jarin, sai su ce ba komai ba ne, suma duk sun fuskanci hakan, kuma ta yi hakuri za su daina kukan zuwa wani lokaci, in ji ta.
To sai dai, Dakta Eziechila Ressie, likita kuma kwararra a fannin yara a babbar asibitin Jabi, Abuja ta ce jarirai kan yi kukan dare ne saboda iskan da su ke shaka da kuma nonon da su ke sha.
Ta bayyana cewar, matsalar kukan dare ne mafi koken da su ka fi samu daga iyaye, musamman masu haihuwar farko.
A bayanin ta, dai daga cikin dalilian da ke sa yara kuka a watannin farko shi ne, shan nono da kuma shakar iska, sai ya zama ba sa iya sarrafa abincin da su ke ci tare da shakar iska a lokaci guda.
Likitar ta ci gaba da bayanin cewa, saboda karancin jikinsu da abin sarrafa iska da abinci, hakan kan yi masu wahalar nunfashi da hade abinci.
Jarirai, a cewar likitar, abinda ke hana su kuka da rana shi ne, idan su ka ci abinci, iyayensu kan goya su suna zagayawa da su tare da rainon su da jijjigarsu har sai sun yi bacci, sabanin da dare. “Su kan goyasu su suna zagayawa da su har jariran su yi gyatsa ko gyashi da rana, amman da dare ba za su iya hakan ba saboda gajiyar ayukkan rana.
“Wani lokacin, bacci yakan dauke iyayen a lokacin da su ke shayar da su nono. Ta ce duk abinda jariri ya ci ko ya sha, to dole ya su sarrafa shi, akasin haka zai sa yara kuka.
Ta kara da cewar, mafi abinda ke haifar da matsalar shi ne, rashin iya yin gyashi da sarrafa abinci da dare sabanin da rana.
Amman su na kara girma da watanni, sai abin ya fara ragewa saboda gabban jikinsu sun fara kara girma tare da saba shakar iska da cin abinci, sai ya zama suna iya yin gyashi da kansu.
Ta ce dubarun shayarwa kan taimaka wurin magance wannan matsalar, ta yanda mahaifiya za ta tabbatar da jaririn ya kama daidai kan nono ba tare da barin yana shakar iska mai yawa ba.