Babban Kuskuren Da Mata Ke Aikatawa Wanda Ke Jefa Su Ga Halaka - Android Pols




Da yawan 'ƴan mata sukanyi soyayya da samari soyayya ta gaskiya wacce har take kaiwa ga basa tsoron bayyana soyayyar da suke yiwa wanda suke so ɗin koda a gaban wanene.


Hakan yasa basa iya ja'inja da wanda suke so a yayin da ya umarce su da aikata wani abu koda kuwa abin ya saɓawa shari'ah.


Hakan yasa wasu daga cikin maza suke tilastawa wacce suke soyayya da ita da ta tura masa hoton tsiraicinta wanda kuma hakan yana faruwa a yau da gobe da jibi, wanda 'ƴan mata da yawan gaske suna aikata hakan.


Da yawan mata masu aikata hakan suna faɗawa cikin mummunar nadama a duniya da lahira.


Shi namiji akan ya sami abinda yakeso a gurin mace yana iya kwantar dakai, yayita ladabi yana lallaɓata, ya rinƙa rarrashinta, ya kuma bata duk abinda takeso, ko kuma yabi mata ta duk wata hanya da yasan tanason hakan da sauransu.


Illar dake cikin tura hoton itace, shi hoton tsiraici na mace yana da haɗari sosai, domin shi wanda kika turawa baki san adadin mutanen dake ɗaukar wayarsa ba.


Sannan kuma koda ya ɓoye sirrinki, ba lallai ya iya ɓoyewa abokinsa na kusa da shi ba, wato amininsa nake nufi, kuma daga aminin nasa hoton yana iya yaɗuwa a duniya, daganan sai ki ganshi har a cikin gidanku an turawa wani ɗan uwanki.


Sannan a shari'ance bai halatta ki turawa namiji hoton da jikinki ba, domin zai iya amfani da wannan hoton wajen cin mutuncinki harma da danginki baki ɗaya.


Sannan kuma baki da tabbas ɗin zai aureki, koda kuwa zai aureki daga lokacin da kika tura masa hoton jikinki, to kimarki da darajarki saita ragu a gurinsa sai dai kawai idan ya ɓoye miki.


Sannan koda kuwa mijinki ne bai dace ki tura masa hoton tsiraicin kiba, domin hoton yana iya fita ya shiga duniya baki sani ba, balle saurayinki.


Sannan kiyi tunani shin idan ke ƙanwarsa ce sai yaga hoton tsiraicinki a wani guri wane irin mataki zai ɗauka akanki, shin zai iya saka ƙanwarsa ta tura masa hoton jikinta?


Kai kuma kaji tsoron Allah duk abinda kasan bakaso kaga ƙanwarka ko 'ƴarka tana aikatawa mara kyau, to kaima kada kasa ƙanwar wani ko 'ƴar wani aikata haka don Allah.


Duk wanda yake saka wata tana tura masa hoton tsiracinta, to ka sani kaima haka za'a saka naka 'ƴa'ƴan su rinƙa turawa nasu samarin.


Kuji tsoron Allah kada ku zalunci 'ƴa'ƴan wasu, kada kuci amanarsu, kada ku cutar dasu idan har kuma bakwaso a cutar da naku 'ƴa'ƴan.


'Yan mata ina kira gareku da kuji tsoron Allah ku nisanci tura hotunan tsiraicinku ga samari domin gujewa faɗawa hadarin duniya da lahira.


Allah ka bamu ikon aiki da abinda muka Karanta. Allah ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post