Jaruma Rahama Sadau ta ƙure adaka a bikin ba da kyaututtuka ga gwarazan 'yan fim na Afrika, wato African Movie Viewers Choice Awards (AMVCA), ƙashi na 9 da aka gudanar a Legas.
A yayin bikin dai an hangi jaruman Kannywood da yawa da suka samu halartar taron wanda aka basu kyautuka daban-daban.
Itama jaruma Rahama Sadau ta halarci wajen cikin wani salon shiga wanda ya jawo mutane musamman daga arewacin Najeriya ke ta yin tsokaci akan shigar da ta yi wacce ake ganin ya saɓa da koyarwar addini da kuma al'ada.