Ƴan Mata Da Samari Kowa Ya Yiwa Kansa Hisabi - Android Pols




Shin idan ka samu matar aure mai irin halinka saka zaka aureta?


• Shin idan kika sami mijin aure mai irin halinki sak, zaki aureshi?


• Duk wanda yake son mace tagari, to shima ya zama nagari.


• Duk wacce take son miji nagari, to itama ta zama ta gari.


• Ba za ka gama zagaye 'ƴa'ƴan mutane ba, kuma kace ba za ka auri wacce aka zagaye ba.


• Ba za ki gama sayar da budurcin ki ba ga samari, kuma ki ce kina son miji nagari ba.


• Duk irin ɗabi'un da kake kai, kaima irin matar da zaka aura kenan.


• Duk irin ɗabi'un da kike kai, kema irin mijin da za ki aura kenan.


• Dan Allah samari da 'ƴan mata mu gyara halayenmu.


• Duk wanda ya canja halayensa ya kuma tuba babu shakka Allah zai gafarta masa ya kuma bashi abokiyar zama ta gari.


•  Duk wacce ta canja ta gyara halayenta kuma ta tuba Allah zai gafarta mata ya kuma bata miji nagari.


Allahka azurtamu da abokan zama nagari.


Allahu kabamu ikon aiki da abinda muka karanta.


Allah ka gafarta mana zunubanmu baki ɗaya Ameen.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post