Idan ana maganar amfanin da lalle ke yi ga jikin dan adam ba za su iya lissafuwa ba saboda yawansu. Idan ana maganar lalle abinda ke zuwan zuciyar mutum shine ado da mata suke yi dashi.
Sai dai akwai hanyoyi da dama da ake yin amfani da lalle da ke inganta lafiyar dan adam kamar yadda zan sanar daku a yanzu. Ga Kadan Daga Ciki kamar haka
1: Ana dafa ganyen lalle ko garinsa da ruwa mace za ta shiga Na mintuna 10/15 hatta karamar yarinya Yar shekara 1 za'a iya saka ta ciki yana maganin infection da cututtuka na mata.
2: lalle yana maganin ciwon hakori da warin baki da kuma tsatsar dake jikin hakora...idan aka dafa lalle da da ruwa sai a rika kuskure baki dashi. Sannan a samu garin lalle da kanunfari da gawayi a daka su tare a ringa goge baki dashi yana kara karfin hakora sosai
3: lalle yana maganin ciwon kafa musamman irin kakannimmu da iyaye jijiya ta rike gwi za'a kwaba lalle a kunsashi a gwiwa sai a rufe da Leda ko bandeji a barshi na tsawon awa biyu ko daya sannan a cire, bayan an cire sai a samu albabulnat a dafa shi a ruwan zafi sai a samu towel a ringa dannawa a kafar sai a hada ruwan kal da zaitun asa garin lalle a hada sai a ringa shafawa a kafar yana magani sosai domin mungwadashi.
4:lalle yana maganin cin ruwa Na kafa idan aka hada lalle da ruwan kal ko afram sai asa a kafar.
5:lalle yana maganin ciwon huhu idan aka samu ganyen danyen lalle guda uku 3 sai a dafashi sannan a saka sugar ko Zuma asha yana maganin ciwon huhu.
6:lalle yana maganin warin kashi da zakaji mutun yana wari da tsami idan a kaje wanka sai aringa dafa lalle a kara wanke jiki dashi yana maganin warin kashi sosai.
7:lalle yana maganin jiri(ajijiya) da mutun yakeyi idan aka dafa lalle a saka Zuma maikyau asha.
8:lalle yana kara karfin farce da maganin tsagewar hannu ( Dan uba) idan aka yawaita saka lalle a hannu ko kafa.
9:Ana Shankar lalle a hanci yana buda kwakwalwa.
10:Ana samun ganyen lalle guda uku ko biyu a jika a Kofi idan ya jiku sai asa sugar asha amma ba'a kara sha sai bayan kwana biyu yana maganin ciwon koda.
11:Ana dafa lalle da Zuma mai kyau a ringa sha yana maganin hawan jini da bugun zuciya wallahi angwada angani.
12:Ana shafawa kuna lalle idan mutun ya kone ko yaji rauni sai a samu kal tuffa a goga agun sannan a barbada garin lalle akai kunar zai kame sosai.
13:Ana samun ganyen lalle guda 20 sai a samu ruwa cikin kwanon shan ruwa daya sugar gram 10 ko 20 a jika a ruwan a ringa sha tsawon kwana 40 yana maganin kuturta insha Allah.
14: yin lalle a kafa yana budewa mace kofofin jini, musamman macen da jinin al'ada yake mata wasa wata biyu ko uku sannan yadawo to wallahi yin lalle a kafa tana magancewa ba sai kin je neman Magani ba ku gwada.
15: lalle yana maganin kurajan jiki daji ( Cancer) idan aka hada lalle da man shanu a ringa shafawa a jiki.
16:lalle yana maganin ciwon Mara ko cikin lokacin da mace take jinin al'ada idan ta samu garin lallen sai ta kada a ruwa ta sha.
17: A samu ganyen lalle guda 3 da furan lalle da Zuma a jika su akofi da ruwan zafi asha yana maganin mura.
18: A hada garin lalle da kal a ringa shafawa akai yana maganin ciwon kai.
19: idan mutun yana habo jini yana ta zuba yaki tsayawa sai a kwaba lalle a dora akan hancin insha Allah jinin zai tsaya.
20: matar auren da tafiya budewa za ta samu lalle ta kwaba da ruwan dumi ta saka a gabanta na tsawon awa biyu sannan ta cire ta wanke da ruwan dumi yana matse mace sosai.
21:lalle yana maganin rauni na ciwon sugar idan mai ciwon sugar yaji rauni yakan dade bai warkeba to idan aka kwaba lalle akasa a gun zai warke insha Allah.
22:a dafa lalle tare da ruwan kal sai a ringa shafawa a baya yana maganin ciwon baya ko kiringayin irin yanda shafawa idan kai yana ciwo.
23:ana shafawa jariri lalle idan anhaifeshi kafin aimasa wanka ashfa masa lalle Na tsawon mintuna biyar ko uku yana maganin cututtuka.
24:Shafa man lalle a karaya yana hade karaya akwai man lalle.
25:ana hada lalle da man wardi ko man lalle ashafawa me cutar barin jiki.
26:ana hada lalle daman kahhh poor ba kafurba sai anja kahhh poor yana maganin sanyin kashi.
27:ganye lalle guda biyu da ruwa Rabin Kofi da sugar tea spoon asha yana maganin shawara.
28:lalle yana Magani karyewar gashi a samu garin lalle katan Kofi da garin habbatussauda cokali 3 da cokali 3 Na ruwan dumi ko a tafasa a shafa akai na awa 3 ko 4 sannan a wanke. Idan kuma gashi bashi da karfi sosai sai a sa lalle rabin Kofi da cokali biyu Na wardi sai ruwa kramin Kofi sai a shafa na awa 1 ko biyu sannan a wanke.
29 Ana hada lalle da Zuma a shafa a gashi yana gyara gashi sosai.
30:Ana hada
Lalle
Zuma
Manja
Hulba
Da kwai
Ashafa a jiki sannan ayi steaming da ruwan zafi (aturara jiki) yana gyaran jiki sosai.
31: ana shafawa gawa lalle yana gyarata.
Wannan shine kwararan bincike da aka yi a kan itaciyar Lalle da fatan za mu gwada mugani.