Alamomi 9 da Zaka Gane Idan Budurwar Da Kakeso Bata Sonka - Android Pols




Akwai wasu alamomi da ya kamata duk namiji ko mace su gane Idan wanda suke soyayya dashi yana son su dagaske ko akasin haka. Ga abubuwan kamar haka :


1. Idan budurwa bata sonka bazata iya kirana a waya da kud'inta ba sai dai tayi maka flashing, don haka iya mutuncin da zata iya yi maka Kenan tayi maka flashin amma bazata taba iya kiranka a waya ba.


2. Idann budurwa bata sonka zata yi ta maka korafi akan kananun bukatunta.


3. Idan budurwa bata sonka toh zata yi maka wasa da dariya da murmushine kawai a lokacin da zaka bata kudi (money), kokuma a lokacin da take so ka bata kudi.


4. Idan budurwa bata sonka toh bazata taba yi maka maganan aurenku da ita ba, ko maganan yadda tsarin aurenku takeso ya kasance ba.


5. Idan budurwa bata sonka toh bazata tabarakabka wani waje ba, kudin da ita zata karba daga wajenka kawai tafiso.


6. Idan budurwa bata sonka bazata ringa baka shawara akan rayuwarka ba, sannan bazata nemi kabata shawara akan rayuwarta ba.


7. Idan budurwa bata sonka bazata taba kawo muku ziyara a gidanku ba.


8. Idan budurwa bata sonka toh bazata taba gaya maka gasakiya akan labarin kanta ba, sai dai ta yita maka karairayi.


9. Idan budurwa bata sonka toh bazata taba yarda ace kakarbi wayanta ka gani ba, saboda akwai lambobin samarikanta da yawa acikin..


Wannan sune wasu daga cikin alamomi 9 da za ka gane macen da kakeso tana kaunarka dagske ko kuwa bata Sonka. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post