Duk mace kana soma tsayar da ita Zaka yi mata magana idanuwan ta tuni zasu auna wadannan abunuwan kafin ma ka gama maganarka. Wadannan abunuwan sune kamar haka:
1:Fuskar Ka.
2: Irin Kwarjinin Ka.
3: Wani Irin Kaya Ne Kake Sanye Dashi
4: Kalar Agogon Daka Daura.
5: Irin Zoben Daka Saka.
6: Irin Tabarau Da ka Saka (Idan kana sanye dashi).
7: Gaba Daya Halittar Ka. Dogo Ne Ko Gajere, Mai Jiki Ne Ko Ramemmene Kai. Ko Kayi Kyau A Shigar Da Kayi.
8: Irin Kalaman Ka.
9: Wani Irin Turare Ka Fesa Ko Ka Shafa.
10: Takalmin Kafafuwan Ka.
11: Motar Ka (Idan a mota ko a abun hawa kake)
12: Fatar Jikinka. Kana Hutawa Ko A Gajiye Kake.
Cikin 'yan dakika har ta gama karance ka, a kuma wannan lokacin za ta amincewa kwakwaluwanta da zuciyar ta ko ta soka ko ta kika.
Don haka kada ka tinkari mace baka shirya ba.