Abinda Ya Haddasa Yakin Sudan Jamhuriyar Musulunci (kashi na uku) - Android Pols




Akwai sojojin haya da na 'yan tawaye har ma da 'yan ta'adda daga Chadi, Kamaru, South Sudan da Nijer wanda suka shiga Sudan suna taya mataimakin Shugaban Kasar Sudan Janar Muhammad Hamdan Dagalo babban kwamandan rundinar Rapid Support Forces (RSF) yaki, wanda dama shi Dagalo asalinsa dan Kasar Chadi ne, kuma tsageri ne gawurtaccen dan daba, ku duba rubutu kashi na biyu da nayi a kansa. 


Misali da abinda ya faru a lokacin Boko Haram a nan Kasarmu Nigeria, inda Boko Haram ta shigo da mayaka daga kasashen ketare suna tayata yaki da Sojojin Nigeria, to abinda yake faruwa a Sudan kenan, hatta Kwamandan yakin Boko Haram wanda kusan shine ya jagoranci karban garuruwan da Boko Haram suka karba a Nigeria  sunansa Mustapha Chadi, dan asalin Kasar Chadi ne, kuma tsohon Sojan Chadi ne ya shiga tawaye kafin ya shigo Boko Haram, a duk cikin mayakan Boko Haram babu wanda ya kai Mustapha Chadi kwarewa a yakin Sahara, daga bisani Shekau ya yaudareshi ya kashe shi a garin Gwoza saboda tsoron zai masa juyin Mulki. 


Janar Dagalo ya tara kowani bangare na mayaka da 'yan ta'adda suna tayashi yaki a Sudan, sannan duk sati guda abinda Janar Dagalo yake biyan Sojojinsa shine Dalar Amurka dubu biyu, duk sati fa, kimanin Naira Miliyan daya da rabi a kudin Nigeria, kuma yana da yawan mayaka sun haura dubu dari, saboda duk Sudan babu wanda ya kaishi kudi, gaba daya cibiyoyin hako ma'adinan zinare na Kasar Sudan yana hannunsa, mai kudi ne na fitar hankali, Shiyasa yanzu haka a Sudan idan Sojojin Al-Burhan suka ji kana magana da harce irin na mutane Chadi kashe ka za su yi. 


Kuma abinda Sojojin Dagalo sukeyi ya koma zallan ta'addanci, cin zarafi da keta hakkin bil'adama, suna fasa shaguna su saci kaya, suna shiga gidan matan aure su musu fyade

Yanzu haka sama da kashi sittin na mutanen dake cikin babban birnin Sudan wato Khartoum sun fice daga garin zuwa neman mafaka, wannan shine sakamakon Zanga-zanga da sukea yiwa shugaba Umar Albashir. 


Wallahi zanga-zanga masifa ne, duk abinda muka ga Allah da Manzon sa sun hana to wallahi abin ba karamin bala'i ne ba, amma haka mutanen mu suke biye wa yaudaran turawa da yahudawa. 


Mutanen Sudan sun shiga cikin yanayi na juyayi da dana sani marar amfani, mutanen Sudan suna da matukar kaunar Kasarsu, amma yanzu gashi suna ji suna gani guduwa suke daga garin kuma da kafa, sakamakon yiwa shugaba Umar Al-Bashir tawaye da zanga-zanga. 


Sun kori Shugaba Al-Bashir wanda yake kare musu martaba da addini, karnukan farautar Amurka suka hau, shiyasa Farkon abinda Janar al-Burhan yayi bayan ya hau kujeran Shugaban Kasa shine cire darasin karantar da Al-Qurani Maigirma da yayi a makarantun boko na Gwamnati kamar yadda nayi bayani a rubutu kashi na farko, yace wai karatun Qur'ani yana hana yaransu fahimtar ilmin kimiyya na zamani. 


Sannan ya shigar da mata cikin harkokin shugabanci, ya fito ya soki hadisin Annabi (SAW) wanda ya hana mata Shugabanci, ya bawa mata cikakken damar yin duk abinda suka ga dama a Sudan, kamar mace ta kama gidan haya tayi zaman kanta, da kama daki a hotel, da bude guraren shakatawa da sayar da giya wanda duk an haramtasu a Sudan lokacin mulkin Umar Al-Bashir, baka isa a ganka da balarabiya kana yawo ba a Sudan sai an kamaka, amma yanzu duk babu wannan. 


Da wahala tayi watala sai mutanen Sudan suka taru suka je bakin gidan yari inda aka tsare Umar Al-bashir suna ta rokonsa ya dawo, yace musu shi bai bukata, shi yanzu yafi jin dadi ma da ya shigo jami'ar Annabi Yusuf, bai da 'yan uwa na jini a duniya duk sun kare, yace kune 'yan uwana amma kuka gujeni, kuma Allahi bai taba bashi haihuwa bai da yaro ko guda daya, daga shi sai matarsa suke a gidan yari suna rayuwa tare, yace duk abinda ya tara na dukiya sojoji sun kwace l, to me ya rage? Yace zamansa anan gidan yari bai iya rike adadin sau nawa ya sauke Qur'ani ba, yace shi Wallahi bai son ya fita daga gidan yari a raye. 


Shugaba Al-Bashir yace da ma na fada muku, sai kunzo kunyi da na sanin tawayen da kuka min, zaku san cewa Amerika sun cuceku, sun yaudareku da Freedom, yace wani irin Freedom kuke nema? baku da matsalar tsaro, baku da matsalar ilmi, baku da matsalar yunwa da kula da kiwon lafiya, baku da matsalar wutar lantarki da ruwan sha, amma kukace wai kuna son 'yanci, kuka min tawaye, ta ga sakamako nan. 


Wani masanin yaki na duniya dan Kasar Sudan, anyi hira dashi a Aljazeera, yace wannan yakin da aka fara a Sudan zai iya kai shekaru 17 kafin a gama Sudan ta dawo kamar yadda take a baya lokacin Umar Al-bashir, halin da Sudan ta shiga ciki Wallahi sai dai gyaran Allah kawai saboda sun taba Allah a cikin lamarin. 


Muna fatan Allah Ya amintar da bayinsa salihai da mata da yara dake Sudan, Allah Ya basu mafita na alheri. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post