Wannan kam al'amari ne mai ban mamaki, kuma da yawa za su iya cewa hakan ba zai yuwa ba. Amma idan kuka dubi hujjojin da zan kawo zaku gamsu da hakan. Yana da kyau me saurare /karatu ya fahimci cewa wannan zato ne kawai. Wato hasashe ne duba da wasu al'kalma da suke gaba na kamar haka:
1. Tsadar kayan Lefe - Bayani daga bakin wanda su kayi aure a 2020 da kuma wanda su ka yi a 2022, ya nuna cewa a 2020 naira 500,000 zata iya yi maka kayan lefe na rufin asiri. Amma a shekarar 2022, naira million daya baza ta maka komai yadda kake so ba.
Saboda yan mata sun saka buri akan lefe. Yanzu yar talaka ma so take kayi mata lefe akwati set uku zuwa abin da yayi sama da haka. Wannan yana nuna cewa nan da shekara biyar masu zuwa, samari baza su iya auren budurwa ba, saboda bukatun ta sun fi karfin talaka.
A yau har ankai ana iya fasa aure saboda kayan lefe, duk da cewa shi lefen ma bai kai kaso 10 bisa 100 na abubuwan da mace zata samu a rayuwar ta ta aure ba. Sun gwammace su rasa miji da su yi hakuri da abinda namiji ya kawo.
Ita kuwa bazawara yanzu akwai su har da kanana. Sai kaga yarinya yar shekara 18, 19, 20, 23, fresh, tana neman miji. Kuma ita sadaki kawai take nema a wajen ka. Idan ka samu yar tarbiyya, wallahi ta fiye maka wannan marasa kunyan yaran masu burin bala'e.
2. Al'adun biki marasa asali - Bayan saurayi ya kai lefe an yi dace sun karba. Babban tashin hankalin sa kuma shine sai a fara jero wasu events, dinner, mothers eve, fathers eve, friends eve, cocktail, gaɗa party, waye party, duk gasu nan iri-iri. Kuma ace dole sai ka yi wasu daga ciki.
A yau mafi karancin abin da zaka iya kashewa a event shine million daya. Idan kuwa so kake a fita kunya, sai ka kashe million biyu da doriya. Kuma idan kace baza ka iya ba, sai ayi ta tsine maka, ana jin haushin ka. Wata ma daga nan zaku fara haurawa da iyayen ta. Shi yasa da anyi aure wata uku sai kaji anyi saki.
Ita kuwa bazawara, dama ita auren ne ya dame ta. Don haka bata bukatar wani event. Idan tayi tsamari tayi walima. Shikenan.
3. Tsirface-Tsirfacen Biki - Ban da lefe da al'adun banza sai kuma kaji yarinya ta fito da wasu tsirface-tsirface na neman kudi. A bada kudin wannan, a bada kudin wancan, kaji abu kamar bazai kare ba. Tun kafin ka aure ta, ta fara nuna maka rashin imani da rashin tausayi. Kawai ita dai ka biya mata bukatar ta, ko mutuwa zakai don rashin kudi ita ba ruwan ta. Toh anan ma bazawara ba ruwan ta. Highest tace ka bata kudin gyaran jiki 30k. Shikenan sai aure.
4. Dogon buri - Yan matan yanzu buri ya musu yawa. Tun baka aure ta ba, ta fara gaya maka plan din ta na rayuwa. Including abin da take ci, abinda take sakawa, abinda bata so da sauran su. Da zarar ta shiga, toh abinda zatayi maka yafi haka.
Ita kuwa bazawara dama ta riga ta shiga rayuwar aure, tasan banbanci tsakanin gaskiya da gaibu. Ita a shirye take ta zauna da kai cikin kwanciyar hankali.
Daga Karshe) Conclusion)
A karshe idan da ka auri yarinya budurwa, sai kaga tazo ta barka da bashi, ga kuma matsalolin ta. Kana fama da biyan bashi, kana fama da sabbin bukatunta.
Don haka ina hango cewa idan mata da iyaye basu gyara wannan matsalolin ba, toh nan ba da dadewa ba, maza zasu fara hijira zuwa wajen auren zawarawa a auren fari. Don haka zawarawa sai ku karkade shimfidar ku ku jira, lokacin ku yazo, zaku fara cin kasuwar samari. Dama auran zawara babbar sunnah ce. Jiya wani abokina ya daura aure da bazawara kuma auren sa ne na farko.