Ni’imar gaban mace ba wai halitta bace wanda za ace wata an halicce ta dashi wata kuwa haka Allah Ya yita Kamas. Kowace mace ita ce ke mayar da kanta mai dadi a wajen mijinta.
1: Soyayya: Duk yadda mace take muddin babu soyayyarta a zuciyar mijinta ba zai taba jin daɗin ta ba ko sau nawa zai kwanta da ita. Don haka danƙon soyayya a tsakanin ma’aurata yana kara saka wa namiji yaji daɗin matarsa a lokacin jima'i.
2: Shauƙi: a lokacin da namiji ya kamu da sauƙin son yin jima’i da matarsa a wannan lokacin yana samun jin dadi na musamman idan yana saduwa da matarsa. Ba kamar lokacin da bai da sha’awar yi ba amma aka nemi yayi.
A lokacin da namiji da kansa yake cikin bukatar matarsa a wannan lokacin idan zai yi jima’i da ita yafi jin daɗin ta.
3: Tsafta: duk yadda miji yake son matarsa kuma yake da shaukin son yin jima’i da ita idan batada tsafta zai dai biya bukatarsa ne amma ba wai saboda yana jin dadi ba.
Matan da suke barin gaban su babu tsafta ko bakin su, hamata da sauran lungunan jikunansu babu tsafta. Irin waɗannan matan namiji ba zai taba jin daɗin yin jima’i dasu ba sai dai kawai ya biya bukatarsa amma ba domin yaji daɗin ta ba.
Ita mace mai tsafta bayaga dadi da take saka mijinta yaji, ta kan kuma sashi a kullum yaji ya kamu da son yin jima’i da ita.
4 :Ni’Ima: ba kowace mace take da ni’ima ba. Wasu matan gaban su a bushe yake karas. Wasu kuwa a jike yake cakaf.
Yawan ni’imar gaban mace yana karawa namiji jin daɗin ta sosai a lokacin da yake saduwa da ita. Wannan yasa maza da dama suke danganta mace mai yawan ruwa a gabanta itace mai dadi.
Shi dai ni’imar gaban mace ba wai halitta bace wanda za ace wata an halicce ta dashi wata kuwa haka Allah Ya yita kamas.
Duk mace tana iya samarwa kanta ni’ima idan tana bukatar yin hakan. Saboda akwai abinci da abubuwan sha da suke sa mace ta samu ni’ima da kuma masu kara mata idan tana dashi.
A lokacin da namiji yake saduwa da mace mai ni’ima wannan ruwan gaban nata yana kara taimakawa wajen samun sauƙin shiga da fita da azzakarin sa ke yi cikin farjin matarsa. Wanda hakan yake samar masa da wani dadi na musamman a lokacin jima’i. Sabanin macen da gabanta yake bushe.
Wanda maimakon ta samar da ɗaɗin tana ma iya jin ciwo a gabanta kuma ta jiwa mijin nata shima. Mazan da matan su suke da bushenshen farji fatar jikin azzakarin su yana iya sullubewa ya daye saboda rashin samun ruwan da zai rika taimakamawa wajen shiga da fita. Wanda ita ma gabanta zai iya yin jini kuma ta rika jin zafi idan ana saduwa da ita saboda rashin ni’ima a jikin ta.
Don haka mace mai ni’ima tafi mara shi dadi a jima’ince.
5: Iyawa: Macen da ta iya jima’i ta kwarai ta kuma saki jiki tafi sabuwar shiga ‘yar koyo dadi a jima’ince.
Domin ba wai kawai a zura azzakari cikin farjin mace bane kaɗai zai samarwa maigida dadi dake kunshe cikin jima’i. Da akwai wasu sinadarori da ake hadawa dasu kafin mace ta samarwa mijinta hakikanin jin daɗin jima’i. Waɗannan abubuwan kuwa suna hada kamar haka:
Iya wasannin motsa sha’awa. Macen da ta iya wasanni da mijinta ba zata taba yin daidai da wacce bata iya ba. Don haka muddin mace ta san abubuwan da mijinta yake son a yi masa a lokacin suna wassanin motsa sha’awa dole ne a wannan jima’in ta jiyar dashi dadi.
Iya yanayin kwanciyar jima’i – dole mace ta iya yin yanayin kwanciya na jima’i daban-daban idan har tana son mijinta ya rika jin daɗin ta.
Kowani namiji yana da yanayin da ya fi so matarsa ta yi masa a lokacin jima’i. Muddin kuma bazaki iya yi masa wannan ba babu yadda za ayi yaji dadinki.
Tsukewa da sakewa: akwai wasu mata yadda aka shige su haka nan suke sakin gaban su ba tare da sun daidaita shi yadda azzakari zai iya samun daidaito a cikinsu. Macen da take da faffadar farji, yana da kyau a lokacin da maigida ya shigeta ta tsuke farjinta yadda zai matsai azzakarin mijin a ciki.
Haka kuma idan karamar gaba ce da ita sai tayi kokarin kara bude kafafuwanta domin baiwa azzakari damar gudanarwa. Wannan yanayin na tsukewa ko matsai farji a lokacin jima’i, yana samar da ɗaɗi na musamman ga namiji. Ba kamar macen da za ta saki komai yadda yake ba.
Sumbatu: Yana matukar karawa maza jin daɗin jima’i sosai amma akasarim mata basu da masaniyar hakan. Sumbatu musamman na kwarzanta mai gida ko yi masa koke-koke na kissa da furta wasu kalamai na batsa suna da matukar tasiri a lokacin jima’i. Domin suna samar da jin dadi na musamman a yayi jima’i. Ba mace ta yi gum bata cewa komai ba.
Tallafawa. A lokacin jima’i ba wai namiji bane kadai mace zata bari yana gwatso ba. A duk irin yanayin kwanciyar da zai baiwa mace damar ta motsa jikinta, to idan za ta tallafawa maigida wannan ma yakan samar da jin daɗi maimakon mace bata motsi ta yi kamar gawa.
Waɗannan sune wasu mahimman abubuwan da zan iya kawo su a fili da suke sa namiji yaji daɗin jima’i da matarsa. Kuma sune suka bambamta mace mai daɗi da mara daɗi.
Da fatan an ilimantu daga wannan takaitaccen bayani, kuma da fatan mata za su yi kokarin gyara yadda suke mu'amalar su da mazajensu.