Yanayi yana faruwa wanda mace zata kasance tana jin zafi a lokacin da ake saduwa (jima’i) da ita.
Hakan yana samuwa ne sakamakon wasu cututtuka da suke damun mace, wanda asalin su suna da asali da tarihin cuta ta dangi, ko kuma cutar dake kama mutum bisa dalilin yanayi na muhalli.
Wani lokacin kuma yanayin abinci da mace take ci, suna da tushe wajen sa mace taji zafi lokacin da Mijinta yake kwanciya da ita.
Saboda haka, akwai hanyoyi daban-daban, wadanda mace za ta bi domin magance wannan matsalar.
Wannan wani hadi ne da ake yi don magance zafin Jima'i ko rashin sha’awa ko daukewar ni’ima.
Abubuwan da Mace za ta nema domin hada wannan maganin sune kamar haka.
(1) Garin Habbatussauda
(2) Garin Ridi
(3) Garin Raihan
(4) Dabino
Bayan kin samo wadannan abubuwan da yadda zakiyi hadin maganin da kuma yadda zaku sha akan ka’ida.
Za’a samu zuma lita daya a hadasu wuri daya, a rinka sha cokali daya a ruwan shayi safe da yamma.
Allah ya bada sa’a ya wuce gaba.