Zazzafar muhawara ta ɓarke a kafafen sada zumunta sakamakon sabuwar waƙa da fitaccen mawaƙin siyasar nan na APC Dauda Kahutu Rarara ya fitar kan zaɓen Gwamnan Kano.
A cikin waƙar dai Rarara ya jaddada furucin Gwamna mai barin gado Dr. Abdullahi Umar Ganduje wanda ya kira sakamakon zaɓen da Tangal-tangal.
Rarara ya kuma yi suka ga jam'iyyar NNPP da jagoranta lamarin da ya fusata mabiyanta musamman a kafafen sada zumunta.
Tun bayan sanar da sakamakon zabe wanda Hukumar INEC ta bayyana Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben Kano ba'a sake jin duriyar mawaki Rarara ba sai yanzu.