Rundunar ƴan sandan jahar Kano ta samu nasarar ta cafke matasan da ake zargi da hallaka wata budurwa mai suna Theresa Yakubu mazauniyar ƙaramar hukumar Bebeji Kano.
Kakakin rundunar ƴan sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana cewa, lamarin ya faru ne a ranar 28 ga watan maris ɗin da ya gabata , bayan an ga wata mata a kwance bata motsi a Garin Anadariya a ƙaramar hukumar Bebeji ta jahar Kano.
Bayan samun rahotanne kwamishinan ƴan sandan jahar Kano CP Mamman Dauda ya tura dakarun ƴan sanda wajen da lamarin ya faru ƙarƙashin jagorancin baturen ƴan sandan Bebeji SP Tamim Wada.
Jami'an ƴan sandan sun garzaya da matar zuwa Asibtin Tiga wanda Likita ya tabbatar da rasuwarta .
SP Abdullahi Kiyawa ya ƙara da cewa a binciken farko da suka fara gudanar wa ,sun gano Sunan ta Theresa Yakubu mai shekaru 20 , wanda kuma kafin ta rasu tana ɗauke da juna biyu na watanni biyu.
A binciken da ƴan sanda suke gudanarwa ne ya kai ga kama wani saurayinta mai suna Philibus Ibrahim mai shekaru 20, dake unguwar Korau ƙaramar hukar Tudunwada Kano da kuma abokinsa mai suna Gebrial Bila mai shekaru 25.
Philibus ya tabbatar wa da jami'an ƴan sanda cewa, juna biyun da ta ke ɗauke dashi nasa ne , kuma sunyi , iya bakin ƙoƙarin su dan zubar da juna biyun amma hakan bai yiwu ba.
Akan hakanne shi da abokinsa suka ɗauke akan Babur , da nufin kaita wani waje dan zubar da cikin , waɗanda suka yi amfani da Mayafinta suka shaƙe mata wuya har ta mutu.
Kwamishinan ƴan sandan jahar Kano ya bayar da umarnin an dawo da su babban sashin gudanar da binciken manyan laifukan kisan kai dake Bompai.