Yadda Za ka Gano Mazakutar Ka Tana Aiki Yadda Ya Kamata Ko Ta Mutu, Ko Da Bakada Aure - Android Pols


'Yan uwa da dama suna tambaya shin taya ne ake gane cewa Azzakari yana lafiya ba tare da an kusanci mace ba, to insha Allah mun kawo muku hanyoyi da za ku iya gane hakan.


Da yawa daga 'yan uwa suna damun kansu tare da daga Hankali cewa suna tsoron kada su yi aure su kasa biyawa mace bukatar su, ta hakan wasu suke fadawa zinace-zinace domin wai su samu gamsuwa kafin su yi aure.


Wanda shi kansa damuwa da cewa kana da matsala ko baka da ita zai iya jefa ka cikin wani yanayi da wani hali mara dadi, saboda haka a rika tambayar abu idan ba'a sani ba.


Da farko abubuwan da za kai duba dasu domin ka gane cewa baka da wata Matsala kuma mazakutar ka tana cikin koshin lafiya shine duba da wadan nan abubuwa kamar haka;


1. Ganin fitar farin ruwa a lokacin fitsari.


2. Jin zafi ko jin kaikai ko ciwo a cikin kwarkwaron mazakuta.


3. Ganin jini ko zare-zare a cikin fitsari


4. Ganin kuraje akan mazakutar ka.


5. Gaban ka yayi wata kala sabanin yadda kalar sa take, duk da dama mazakuta tana da duhu fiye da fatar jiki.


6. Ga masu aure akwai jin zafin gaba a lokacin saduwa ko bayan saduwa.

 

Daga cikin alamomin nan da muka bayyana akwai alamomin ciwonn sanyi na bacterial infection kamar su gonorrhea Chlamydia Hpv Virus da sauran su, wanda suna daga cikin abubuwan da suke jawo mazakutar mutum ta samu matsala.


Bayan wadannan akwai wasu abubuwa da suke jawo kaga gaban ka kamar baya yin aiki sune kamar haka;


1. Damuwa Musamman akan lafiyar gaba, ko wasu sha'ani na rayuwa.


2. Rashin kwarin giwar cewa lafiyar ka kalau.


Bayan wannan akwai matsaloli kamar haka ;


1. Kiba mara musaltuwa


2. Ciwon suga


3. Hawan jini


4. Damuwa


5. Wasu ma ciwon zuciya.


Sannan yin masturbation da yawa wato istim’nai shima yana jawo Azzakari ya samu matsala mai girma.


Hanyoyin da za ka bi ka zauna da mazakutar ka lafiya kalau;


1. Daina shaye-shayen Taba da Giya.


2. Yawan motsa jiki


3. Daidaita abinci


Sannan idan baka gane wani abu ba ka tuntubi likitan ka cikin gaggawa ko kuma idan kaga wata alama da muka bayyana.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post