Babu abinda yafi mutuwar aure musiba da tashin hankali a rayuwar aure musamman ga 'ya mace.
Duk lokacin da naga bazawara hankali na kan tashi saboda tashigo wata sabuwar rayuwa wacce bata saba da ita ba. Babbar musifar da bazawara zata fara fuskanta itace ɓullowar samari da zawarawa kamar ruwa, wanda kaso casa'in cikin ɗari ba don Allah suke sonta ba.
Da yawan su suna zuwa ne domin su tattaɓa jikin ta ko kuma su yi zina da ita domin biyan buƙatarsu, saboda su a tunanin su ai ta saba da kwanciyar aure yanzu kuma gashi ta rasa wannan damar.
A wannan lokacin ne za tayi ta cin karo da mazajen bariki tare da samarin zamani suna yi mata kyauta tare da bata kulawa kamar gaske daga nan kuma sai su hure mata kunne a shiga wani sabon babin na daban.
Allah ne kaɗai yasan adadin zawarawan da suka afkawa zinace-zinace tare da yawon bariki sakamakon yaudarar ƴaƴa maza. Da zarar ance ga bazawara nan to a wannan lokacin za kayi ta ganin gantalallun mazaje da mayaudaran samari kowa yana kai caffar sa wurin ta domin neman sa'a.
Da yawan zawarawa hankalin su kan gushe, karasa inda tunanin wasu ya tafi da wayonsu, saboda yadda shedan ke saurin yi musu huɗuba su karɓa.
Yakamata ƴan uwa na maza muji tsoron Allah saboda munfi matan laifi, sannan mu tuna da cewar zawarcin nan ƙaddarace za ta iya faɗawa kan kowa, wasu mazajensu ke mutuwa wasu kuma ƙaddarar aure ce idan tazo sai an rabu.
Idan ka dauwama a lalata rayuwar zawarawa to yakamata kasani kaima fa kana da mata ko ƴa ko uwa ko ƙanwa kuma babu wacce bazata iya samun kanta a zawarci ba, kuma wallahi duk abinda ka yiwa ƴar wani ko uwar wani kaima sai an yiwa naka.
Mu tausayawa zawarawan nan mu basu kulawa ta musamman muma sai Ubangiji ya bamu kulawarsa, dukkan inda ƴa mace take komai ƙanƙantar ta uwace mu girmamata mu ɗora su akan madaidaitacciyar hanya, kada mu saka su kan hanyar da rayuwar su za ta watse.
Muna roƙon Ubangiji ka kawowa zawarawa ɗauki, ka basu mazajen aure nagari ka tsaresu daga sharrin mazajen zamani