Yadda Ake Gamsar Da Mace Lokacin Saduwa - Android Pols


Gamsar da mace lokacin saduwa yana karawa namiji kwarjini a wajen mace akasin haka kuma yana kawo raini wanda wannan ba dabi'ar gwarzon namiji bane domin shi ya kan yi kokarin magance duk wata matsala da zata hanashi gamsar da iyalansa, matsalar daga wurinsa ne ko daga wajen matarsa.


Nasara ko faduwa ba ta samun namiji sai da sahalewar mace, mace itace alkiblar namiji komai jarumar sa itace rauninsa, kuma domin samun daraja a wajen ta dole sai namiji ya zama gwarzo wanda yake rike da kalar zuciyarsa ba wai wanda zuciyarsa ke rike akalar saba.


Wannan shine gwarzon wanda akidarsa itace shimfida rayuwar farin ciki da abokiyar rayuwarsa wato matarsa, Jarumin yasha alwashin cimma burinsa ta hanyar yiwa rayuwarsa tsari me kyau Har saida takai kafin aurensa ya samu komai na jin dadin rayuwa a tunaninsa mace ta gari itace kadai bukatarsa a wajen Allah sai kuma gashi allah ya amshi addu'arsa, to saidai kash abunda akaso ya faru ba shine ya faruba bayan anyi aure nanfa wannan jarumin ya sake fahimtar hankali ba zai taba kwanciyaba har sai anyi farin ciki da iyali shikuwa farin ciki da iyali ba zai taba samuwa ba har sai an magance matsaloli a bangaren kwanciya.


Na kirashi da gwarzon namiji ne saboda shine mutum na farko da yayi tattaki har sai da takai ga ya ketare I yakar kasar sa ya shiga wata kasar domin magance matsalolin iyalinsa wanda a cewar mata wannan ba dabi'ar maza bane suna ganin matsalolin aure na mata ne harma suna ganin idan namiji yaga mace ta kasa gyara matsalarta tofa Zabi biyu zai bata kodai ya kara aure ko kuma tasan yanda dare yayi mata amma a yau wannan jarumin ya karyata wannan hasashen yayi kaca kaca da kundin shi kadai ya samara gidansa da matarsa farin ciki.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post