Nasiba bint Ka'b (Da Larabci: نسيبة بنت كعب بن عمرو , wanda aka fi sani da Umm 'Umāra (Da Larabci: أمّ عُماره ), ta kasance daga cikin sahabban Manzon Allah (SAWW) mata. kuma Ana kiranta Nusayba.
Tana daga cikin mutanen farko da suka musulunta a madina kuma tana daya daga cikin mata biyu da suka musulunta a yarjejeniya ta biyu ta Aqaba.
Ummu Umar ta halarci wasu Yaƙe-yaƙe musamman yakin Uhudu domin taimakon wadanda suka samu raunuka da mayaka. Ta kuma raka rundunar musulmi a wasu Yaƙe-yaƙe da Wasu abubuwan da suka faru. Ta ruwaito hadisi daga Manzon Allah (SAWW).
Babu wata Ruwaya dangane da lokacin rasuwarta a cikin madogarar Tarihi, amma a wata ruwayar Ance tana raye har zuwa zamanin khalifancin Sayyadina Umar Ibn al-Khattab (RA).
Zuri'a
Mahaifinta shi ne Ka'b ibn Amr daga Banu Mazin, dangin Khazraj sananniyar kabilar Yathrib (Madina) kuma mahaifiyarta ita ce Rubab bint 'Abdullahi, Sun fito daga kabila daya. Don haka ita ma ake ce mata Nasiba al-Maziniyya.
'Ya'yan Ummu Umara biyu, 'Abdullahi da 'Abd al-Rahman ibn Ka'b, suna cikin sahabban Manzon Allah (SAWW).
Aure
Da farko ta auri Zayd ibn 'Asim daga Banu Najjar dangin Khazraj ta haifa masa 'ya'ya biyu da mai suna Habib shi ya sa ake ce mata Umm Habib da 'Abdullahi, wadanda suke cikin sahabban Annabi. Bayan rasuwar mijinta, bayan ta musulunta ta auri Quziyya ibn Amr daga Banu Najjar. Ta haifa masa 'ya'ya biyu, Tamim da Khawla.
Musulunta
Tana cikin mutanen farko da suka musulunta a madina kuma ance tana daya daga cikin mata biyu da suka musulunta a yarjejeniya ta biyu ta Aqaba.
Shiga cikin Yaƙe-yaƙe
Ummu Umar ta halarci wasu Yaƙe-yaƙe musamman ma Yakin Uhudu domin taimakon waɗanda suka samu raunuka. Lokacin da ta ga Manzon Allah (SAWW) yana cikin hatsari a lokacin Yaƙin Uhudu ta ba shi kariya kuma ta samu raunuka masu yawa, don haka Annabi (SAWW) ya yaba mata sannan ya ziyarce ta. Duk da cewa ba za ta iya shiga yakin Hamra'ul Asad ba saboda raunukan da ta samu, ta raka rundunar musulmi a wasu Yaƙe-yaƙe da suka haɗa da yaƙe-yaƙen Khaybar da Hunain.
Ummu Umar kuma ta halarci yakin Yamama, wanda ya faru a zamanin Halifancin Sayyadina Abubakar (RA), kuma ta rasa daya daga hannunta a wannan yakin.
Ummu Umar ta ruwaito wasu hadisai daga Manzon Allah (SAWW).
Mutuwa
Babu wata Ruwaya dangane da rasuwarta a cikin madogarar Tarihi, amma an samun ta daga wata ruwaya cewa tana raye har zuwa zamanin khalifancin Sayyadina Umar ibn al-Khattab (RA)