Shahadar Shiekh Ja'afar Mahmud Adam - Android Pols




A Rana mai Kamar Ta Yau 13 Ga Watan Afrilu 2007 Wanda Yazo Dai-dai Da Ranar juma'a 26/Rabii'u Awwal/1428 Allah Ya Karbi Rayuwar Shiekh Ja'afar Mahmud sakamakon harin da wadansu 'yan ta'adda suka kai masa, a dai-dai lokacin da yake jagorantar sallar asuba a masallacin Juma'a na Dorayi.


Ya rasu ya bar mata biyu, da 'yaya shida, yayin da aka haifa masa ta bakwai kwanaki 58 dai-dai bayan aiwatar da wannan kisan gilla a kansa.


Dubun-dubatar mutane ne daga ko'ina cikin kasar nan suka halarci jana'izarsa, kuma an binne shi ne a makabartar Dorayi.


Baiwa 11 Da Allah Ya Yi Wa Marigayi Sheikh Ja'afar Yayin Rasuwarsa.


1. Shahada: Ya yi Shahada iri daya da ta Sayyidina Umar (R.A).


2. Ya Rasu Ranar Juma'a: Rasuwar Ranar Juma'a Alama ce da ake kyautata wa Mutum zato ya samu dacewa.


3. Mahaddacin Alkur'ani ne: Ana kyautata zaton duk wanda ya haddace Alkur'ani Mai Girma ya kuma kiyaye shi ya yada shi. Zai samu rabauta Ranar Lahira.


4. Kisan Gilla: Duk Muminin da aka yi wa kisan gilla ana sa ran laifukan sa sun rataya a wuyan wanda ya kashe shi.


5. Ya cika da kalmar Shahada: Kafin rasuwar sa an ji shi ya na maimaita kalmar La ila ha illallah Muhammadur Rasulullah


6. Dandazon Mutanen da suka halarci jana'izarsa: Ana kyautata zaton duk mamacin da mutane 40 suka halarci jana'izarsa wadanda ba sa shirka zai samu dacewa.


7. Ya rasu ya na Sallar Asuba. Sallar Asuba na daya daga cikin Sallah mai madaukakiyar daraja.


8. Limami ne shi: Jagorancin Sallah wata babbar baiwa ce da ke kusanta Bawa zuwa ga Allah.


9. Ya Karanta Suratul Al-Maʻārij المعارج,: Kafin a kai ga kashe shi ya karanta sura daga cikin Alkur'ani Mai Girma.


10. Ya Dago Daga Sujada: Sai bayan da ya dago daga sujada sannan makisan sa suka fara harbin sa.


11.Ya Nemi Gafarar Mutane Kafin Rayuwar sa. (Duk wanda na yi wa wani  ba daidai ba don Allah ya yafe min).


Kafin rasuwarsa, malam ya fara gagarumin aikin rubuce tafsirinsa a harshen Hausa a karkashin cibiyar (Sheikh Ja'afar Islamic Documentation Centre).


Ya Allah Ya Jikan Sheikh Jafar Da Rahama Amen 


Ya Allah Ya Kyautata Zuri’arsa Masu Albarka Amen 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post