Masarautar Hausa ta Kano ta kasance a kan Dutsen Dala. Yayin da a baya akwai kananan masarautu a yankin, kamar yadda littafin tarihin Kano ya nuna, Bagauda, Da Bayajidda, ya zama sarkin Kano na farko a shekarar 999, ya yi sarauta har zuwa 1063.
Shi ne mutumin da masana tarihi suke fara lissafin sarautar Kano daga kansa; wato ke nan shi ne Sarkin Kano na farko. Bagauda
Daud Dan Bawo, wanda aka fi sani da Bagauda ko Yakano, shi ne Sarkin Kano na farko, wanda ya yi sarauta daga shekarar 999 zuwa 1063. Ya kafa daular da za ta ci gaba da mulkin jihar sama da shekaru 800. Bisa ga littafin tarihin Kano, duk Sarakuna da Sarakunan Kano da suka biyo baya sun fito daga gare shi.
Shi Bagauda sunan mahaifinsa Bayajida wanda shi kuma Bayajiddan ɗa ne ga sarkin Bagadaza (Baghdad); wacce take cikin Ƙasar Iraƙ a yau.
Shi ne mutumin da masana tarihi suke fara lissafin sarautar Kano daga kansa; wato kenan shi ne Sarkin Kano na farko.
Bagauda ya je garin Kano sanadiyar gudunmawa da su jama'ar ta yankin Kano suka nema daga gurin sarauniya Daurama saboda adabbarsu da mahara suka yi.
Kafin zuwan Bagauda ya mulki Kano dukkan yankunan nan ba a matsayin abu guda suke ba. A’a, akwai gugun jama’ar da ke zaune a kan Dutsen Dala Da Fanisau Da Dutsen Magwan waɗanda suke ƙarƙashin gadon shugabancin Barbushe da kuma sauran jama’ar da ta ƙunshi manoma, mafarauta da sauransu da ke zau ne a Maɗatai.
Abinda ya raba tsakanin waɗannan al’umomi guda biyu kuma shi ne kogin jakara. Haɗewar waɗannan jama’a biyu ƙarƙashin mulkin Sarki guda wato Bagauda, shi ne tushen masarautar Kano.
Babbar nasarar farko da sarki Bagauda ya samu a Kano itace ta ganin bayan shugabannin jama’ar Dala masu bautar Tsimbirbira, daga cikin waɗanda Bagauda ya halaka akwai Jankare, Biju, Bodari da Ribau. Kisan waɗannan manyan matsafa kuma jarumai ya girgiza duk wani mai bautar Tsimbirbira da haka suka sallama suka bishi, sannan kuma a taya ɗaya ɓangare ya tsorata waɗancan baƙin mahara masu zuwa suna yaƙar jama’a mazauna yankin Maɗatai saboda haka ƙasa ta zauna lafiya abubuwa suka ci gaba da tafiya kamar yadda ake so.
Samuwar wannan zaman lafiya ta baiwa Sarki Bagauda cikakkiyar damar ɗaura ɗamarar fita wajen dan faɗaɗa gari ta yankin Arewa. Tun da ya tashi daga gurin da ya zauna na ƙarshe wanda kuma a nan yafi daɗewa, wato Gazarzawa, yaketa fafatawa har sai da ya dangana da Sheme wacce ita ce Kazaure a yau. Tun kafin nan, sarki Bagauda ya fara zama a Durami sannan ya koma Talautawa sannan daga ƙarshe ya koma Gazarzawa kafin barinsa garin. Saboda haka babu wani takamaiman guri wanda Bagauda ya zauna ya kafa fadar mulkinsa a Kano.
Saukar Sarki Bagauda a wannan gari na Sheme, sai ya dira a kan manyan gari, waɗanda suka yi tauri kai kamar irinsu Gubusani, Bauri, Gazawuri, Ɗangefe, Fasataro da Baƙin-bunu duk ya markaɗe su. Saura kuma da suka ga haka ta faru da manyan jarumai sai suka miƙa wuya suka bishi.
Shi Sarki Bagauda wannan sabon zango a wurinsa ya dace saboda ya koma kusa da mahaifiyarsa wanda masana tarihi ke ganin ma cewa ya riƙa samun tallafin mayaƙa daga hannun mahafinsa dan haka ya gagari kowa. Su kuma jama’ar Kano musamman attajirai, manoma, maƙera da sauransu dake zaune a yankin Maɗatai suna ganin Sarki ya yi musu nisa saboda haka suka aika masa da ya taimaka ya dawo gare su duk da cewa basa samun wata barazana daga ciki ko wajen gida.
Wannan gari na Shema a nan Bagauda ya zauna ya ci gaba da hayayyafa har zuwa ƙarshen rayuwarsa.
Iyali
Mahaifin Bagauda shi ne Bawo (wanda kuma Aka rubuta Bauwo). Bagauda yana da ɗa, Warisi , da Saju. Warisi ya gaji mahaifinsa a matsayin sarki a shekara ta 1063.
Akwai tarihin Bagauda daga fassarar littafin Kano Chronicle na Palmer a 1908 a Turance (Mai So Sai Ya Nema)
Madogarar Wannan Rubutu
Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.
Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Saɓannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.
Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.
Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.
Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.
Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Cop, No. 27/32, Beirut Road, Kano.
William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.