Duk mai fama da Ulcer kar yayi wasa da wannan fai'ida. Domin wannan maganin da zan bayyana muku sadidan ne an yi amfani dashi kuma yai aiki sosai.
Duk matsalar ka da Ulcer, duk takurin ka da ulcer duk yadda ulcer ta takura maka, ko da tana hana ka cin wani abu.
Kamar mai sa ciwon baya
Ko ciwon ciki
Ko zafin jiki
Ko zazzabi
Ko kashin majina
Insha Allah wannan fa'ida za ta magance maka matsalar ulcer.
Abinda Za'a ku Nema guda 3 ne kacal kamar haka:
1. Cabbage (Kabeji) musamman jan kabeji
2. Garlic(Tafarnuwa)
3. Zuma
Bayan duk kun samu wadannan abubuwan da na ambata ga kuma Yadda Za'a Hada kamar haka:
Da farko za ku samu kabeji danye ku yayyanka kanana ku debi kamar cikin hannu sanna a samu Tafarnuwa kwayoyin ta guda 2 a samu ruwa kofi 1 sannan a samu blender(abin markade).
Sai a zuba ruwan kofi daya a ciki a zuba kabejin a ciki da kuma Tafarnuwa sai ayi blending nasu (a markada), a juye a kofi sannan a zuba zuma chokali 5 a ciki asha da safe kafin aci komai.
Insha Allah idan akai na tsawon sati 1 za'a samu waraka, Indai matsala ce akan ciwon ulcer za ku rabu da ita gabaki daya.
Idan kun gwada kun samu nasara sai ku yi kokarin sanarwa da sauran yan uwa wanda suka fama da matsalar wannan ciwo na ulcer.