Zuwa ga Shehin Malam mai Tsangayar zamantakewar rayuwa. Muna karuwa da wannan makarantar taka matuka fiye fa yadda kake tunani. Allah Ya biyaka Ya kara basira.
Wata matsala gareni da nake fama da ita nake kuma neman shawararka harma da na daliban wannan makarantar mai albarka.
Yau kusan watannin 7 kenan da yin aure amma na fahimci bana iya gamsar da matata duk kuwa da kusan duk dare idan har muna lafiya muna saduwa kamar sau biyar zuwa 6. Akwai ma lokatai da mukanyi da rana idan wani abu ya dawo dani gida amma duk da haka bayan mun gama zanga kuma tana wasa da gabanta saboda bata samu gamsuwa ba hakan ya soma sani damuwa ko harija na aura ne? Gashi kuma ina matukar sonta banason na rabuda ita. Akaramakalla ko akwai wasu shawarwarin da za a bani yadda zan gamsar da matata?" Daga dalibinka na boye:
Amsa Daga Malam.
Irin wannan wasikun na maza da mata muna samunsu soasai wanda wannan matslar tana daya daga cinkin manyan matsalolin da suke kashe auratayya. Inda namiji zai auro matar data fi karfinsa ko mace ta auro namijin dayafi karfinta a jima'ince wanda daga bisani sai su kasa zaman aure dole suke hakura da junansu su kashe auren.
Saboda yadda maza suke samun kansu cikin wannan matsalar muke ganin ya dace muyi bayani akan harijancin mata a wannan karon.
Da yake mun soma da wasikar maza ne,wannan ya kawo lokacin da za muyi magana akan Harijar mace ( Nymphomaniac). Su wanene mata Harijai. Yaya ake ganesu, yaya ake gamsar da su, da kuma sanin ko suna warkewa daga wannan matsalar.
Wacece Harijar Mace?
Harijar mace ko Nymphomaniac a turance sune Matan da suke da yawan bukatan na jima'i.
Matane dake da karancin gamsuwa na jima'i.
Sune matan da a kullum kuma ako yaushe suke da bukatar ayi jima'i dasu. Matane da sunyi sha'awa nan take suke soma diga, suke fita saga hayyacinsu. Idanuwansu rufewa yake har sai sunji namiji a jikinsu. Matane da suke yawan son wasa da gabansu amma bincike ya nuna basu cika sha'awar yin madigo ba.
Mene ke Jawo Harijancin Mace?:
Malamai na jima'i sun tafi akan cewa halittace.
Amma likitoci harma na addini sun gano cewa mace na iya zama harija ta dalilin abincin da take ci ko take sha. Su kuma masana dabi'ar Dan Adam sunce zamantakewan mace harija yana faruwane irin natsuwa da kwanciyar hankalin da take samu ko take dashi haka bukatanta na jima'i yake karuwa.
Suka kara da cewa mace na iya zama Harija muddin ta soma rayuwanta na jima'i da namijin da yake da matukar sha'awar jima'i kuma ya horas da ita akan hakan. Sukace macen da sama da maza biyu suka mata fyade akwai yiwuwar ta kamu da matsalar Harijanci.
Wadannan sune zantuntuka masu inganci akan harijancin mace.
Ko Ana Iya Gane Harijan Mata?:
A zahiri yanada matukar wahala daga ganin mace ka iya tabbatar da harijace muddin ba ka samu yin kusanci da ita na yadda zaka iya tabbatar da hakan ba, duk kuwa da wadansu masana mata sun siffanta mata harijai masu jajayen idanuwa, masu girman baki, mata masu girman jiki ko masu katon kai. Duk wannan sharshi fadi ne kawai babu wani tabbas domin ana samun mata harijai ako wani irin siffa.
Ita kanta mace bata iya sanin ita harijace har sai idan tana Jima'i. Amma taba yin Jima'i bazai tabbatar da mace harija bace domin kamaceceniya da Harijanci da jaraba suke da shi.
Sai dai abunda ya tabbata sune, budurwa mai karancin shekaru bata iya fahimtar harijancinta har sai tayi aure tana zaman aure koda kuwa tana zina a wajen. Don haka mata harijai sunfi yawa ne cikin matan da suka taba aure kuma wadanda shekarunsu ya soma haura 35 a wannan lokacin ne mace take iya tabbatar da ita harijace ko kuma jarabenbiyace ita.
Shi yasa idan namiji yazo neman wacce ta taba aure, kada yaji nauyi ko kunya tambayan bazawaran tasa dabi'unta a jima'ince domin sanin ko zai iya zama da ita kuwa ya kama gabansa. Hakan yanada matukar alfanu domin gudun kada ayi auren da bazai samu tsawon rai ba.
Ta Yaya Ake Gamsar Dasu?:
Gamsar da Harijar mace a jima'ince ga wanda ba hariji bane ba sauki gareshi ba, muddin ya biyemata da jima'i zai iya cutar da rayuwar sa.
Abunyi bayan ka gano harija ka auro kuma kana sha'awar ci gaba da zama da ita shine zama na fahimtar juna ya kamata ku yi. Ka tabbatar mata kuna da bambamci sha'awa ta fahimci hakan. Ta kuma sausauto da nata sha'awar domin ku samu matsaya.
Idan sau hudu take so a dare sai ta daure ta hakura da biyu saboda soyayyar da take maka. Haka kuma ku tattauna akan abubuwan da take bukata a lokacin da kuke jima'i da ita. Da abubuwan dake sata sauri da kuma saukin gamsuwa.
Duk wani abu da tasan idan za kai mata zai sa ta gamsuwa ba sai lalle shigar azzakarinka cikin farjinta ba su zaka maida hankali akansu. Mata harijai da sauran wasu matan ba wai yawan kawo maniyinka a farjinsu shine yawan gamsar dasu ba.
Kowacce mace da akwai hanyar da take samun gamsuwa haka itama Harija, lakantar hanyoyin gamsar da ita sune hanya kadai mafi sauki da namiji zai samu galaba a kanta musamman idan da kanta ta fadamaka kuma ta nunamaka ta koya maka yadda tak eso kai mata ko a taba mata.
Ko Matsalar Harijanta Yana Da Magani?:
Kamar yadda karancin sha'awa yake da magani haka shima matsala na harijanta yake dashi. Duk da wasu na ganinsa a matsayin halitta ne, kamar yadda wasu ke daukarsa a cuta, akwai magungunan da idan mai wannan matsalar ta ziyarci likita ana iya bata magungunan da zasu rage mata sha'awar jima'i dai-dai gwargwadon bukatarta.
Ita harija ko hariji muddin ba Jima'i suka yi suka fahimci kansu ba yana da wuya a ita bambamta masu wannan halitar da kuma jarababbu. Domin harijanci daban ita kuma jaraba daban.