Mercy Aigbe ta sa masu amfani da soshiyal midiya yamutsa gashin baki bayan bayyanan wani bidiyonta da ya yadu.
Ku tuna cewa jarumar da mijinta, Adekaz sun gayyaci abokai, abokan sana'a da yan uwa zuwa taron Ramadan.
Bayan nasarar da ta samu a taron, an yi hira da jarumar inda ta tabbatar da cewar ta bar addinin kirista zuwa na Musulunci.
A bidiyon, an iya gano jarumar tana sake gabatar da kanta da sunayenta da suka hada da na Musulunci.
Kalamanta:
"Sabon sunana shine Hajia Meenah Mercy Adeoti. Meenah."
A kwanakin baya, mun kawo muku yadda jarumar, Mercy Aigbe ta koka kan yadda rayuwarta ke tafiya a matsayin matar musulmi musamman a wannan wata na Ramadana.
Mercy ta ce ta fara sabawa da azumin Ramadana amma babban kalubalanta shine tashin asubahi don shirya sahur domin a cewarta sam bacci baya isarta kuma hakan kan sa duk sai ta ji ta gaji.