Kwararriyar Likita a fannin lafiyar al'umma Dr Zahra Zambuk Umar ta bayyana Muhimman abubuwan da ya kamata duk mai azumi yai amfani dasu da zarar ansha ruwa.
Abinda ake so mutum ya ci bayan shan ruwa, shine ana so a fara cin Dabino, idan babu sai a sha ruwa da kuma kayan marmari (fruits) da kayan ganye(vegetables).
Yin bude baki da kayan marmari (fruits) da kuma kayan ganye (vegetables) na taimakawa wajen dawo da karkashin jiki. Shan ruwa yana da matukar muhimmanci a lokacin da aka yi bude baki, domin shi ruwa yafi dukkan wani nau'in lemo muhimmanci a lokacin.
Dr Zumbuk ta ce, ana son a sha ruwa mai saukin sanyi ba mai kankara ba an fi son mutum ya sha ruwa mai dumi domin hakan zai taimaka muku wajen warware hanji da saukaka cin abinci.
Dr Zahra ta bayyana irin illolin dake tattare da shan ruwan sanyi, ta ce shan ruwan sanyi a lokacin shan ruwa yana jawo motsewar hanji wanda ke hana abinci saurin narkewa wanda ba zai taimakawa jiki ba.