Matsalar Saurin Inzali Da Hanyoyin Da Za'a Magance Ta - Android Pols




Ko ka san kashi 30 cikin dari na maza na fuskantar wannan matsala ta saurin kawowa maniyyi yayin saduwa da iyalinsu?


To abin haka yake, kamar yadda aka wallafa a mujallar "The journal of the American medical association" Sai dai abin damuwa anan shine duk da matsala ce da ke ciwa maza da yawa tuwo a karya, amma tattaunawa akan ta yakan zama wani abun damuwa, ba don komai ba, sai don al'adarmu, da mu ke daukar al'amura a matsayin na kunya ne koda ba na kunyar bane.


Wannan dalili ya sa mu rubuta makala akan wannan matsala don taimakawa masu fama da matsalar saurin inzali. Ba wani abu ya sa mu yin hakan ba sai don matsala ce da ke haifarwa mai ita matsananciyar damuwa. Mai irin wannan matsala na ganin ya gaza wajen biyawa iyalinsa bukatarta ta jima'i wanda hakan ka iya haifar musu da gagarumar fitina a rayuwar aurensu.

         

Me Ake Nufi Da Saurin Inzali ?

A takaice saurin inzali na nufin zuwan maniyyi da wuri ba lokacin da ake so ba. Mutum zai kasance mai saurin inzali idan yana fitar da maniyyi kafin ko da zarar ya shigar da azzakarinsa cikin farjin iyalinsa. Kai a wani lokacin ma ya kan yi inzalin ne tun lokacin ana gabatar da wasa.


Ita kuwa matsala ce da ke da ban haushi da ban takaici don kuwa tana hana miji da matar samun jin dadi da gamsuwa daga jima'i. Ko da yake masana a wannan fanni sun bayyana cewa wannan matsala ba abar damuwa ba ce tunda akwai hanyoyin magance ta. Kuma sun ce a wasu lokutan takan tafi bayan wani lokaci, amma dai bin wasu mataikai don gusar da ita da sauri zai taimaka.


Wannan matsala ta saurin inzali kan haddasawa ma'aurata jin haushin juna da kawo sabani a tsakanin su musammanma a lokacin da suka zo kwanciya.


Ana sanya mutum cikin masu saurin inzali idan: 

Yana kawo maniyyi minti daya ko kasa da haka da fara saduwa da iyali.

Idan ba zai iya dakatar da inzali ba yayin da yake saduwa da iyali.


Idan hakan ya haifar masa da matsananciyar damuwa da har ya ke gudun yin jima'i.


Me Ke Haifar Da Saurin Inzali ?

Dalilai da yawa ne ke haifar da wannan matsala, don haka babu wani abu guda daya da za'a danganta shi da saurin inzali don kuwa yana danganta ne daga mutum zuwa mutum.


Ga wadansu daga ciki, wadanda kuma su ne suka fi shahara wajen haifar da wannan matsala.


1. Sabon Shiga.

Idan mutum sabon shiga ne, barawo da sallama, Inji hausawa. Ga dukkan alamu wannan baya bukatar karin bayani. Amma dai muna nufin ango farkon aure.


Kasancewar sa sabo ga al'amarin bai san yadda zai mallaki kansa ba yayin saduwa da amarya.


2. Matsananciyar Damuwa.

Idan mutum ya samu kansa cikin damuwa, sakamakon al'amuran rayuwa, hakan kan haifar masa da matsala ta saurin inzali. Wannan kuwa ya hada da damuwa akan basussuka, gidan haya, matsalolin iyali, rashin lafiyar makusanci, durkushewar kasuwanci da dai sauran matsalolin rayuwa.


3. Daukar Lokaci Ba Tare Da Saduwa Ba.

Idan magidanci ya dauki lokaci mai tsawo ba tare da ya sadu da iyali ba, hakan kan haifar masa da saurin inzali.


4. Tsoro.

A duk lokacin da mai gida ya je wa iyali a lokacin da yake tsoron wani abu a rayuwa, ko kuma ya karaya akan ba zai iya biya mata bukata ba, to labudda yana iya kawo maniyyi da wuri.


5. Zumudi.

Wani lokacin idan mutum ya kasa mallakar kansa game da jima'i, saboda wani dalili to zai iya kawowa da wuri.


6. Gaggawa Yayin Jima'i.

Wanan na nufin mai gida ya dinga kaiwa da komowa cikin sauri a yayin jima'i. Ba shakka hakan na sabbaba saurin inzali.


7. Rashin Abinci Mai Gina Jiki.

Kullum dai muna fadar abincinka maganin ka, masana na yawaita bada muhimmanci akan abincin da muke ci don kuwa shi ya shafi dukkan al'amuran lafiyarmu ne.


Fadakarwa: Wasu dalilan da ke haifar da saurin inzali cuta ce ko kuma wacce aka haifi mutum da ita. Ita kam irin wannan sai mai ita ya je ga likita don samun mafita.


Hanyoyin Magance Saurin Inzali.


Babban abin farin ciki game da wannan matsala shine, ana samun bakin zaren cikin sauki matukar dai ango ko magidanci zai bi shawarwarin masana.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post