Idan Zaka yi hira da saurayi da budurwa wadanda suka kamu da soyayyar juna, suna iya ce maka zasu iya rayuwa ako wani irin yanayin da suka samu kansu.
Irin wadannan masoyan suka bijirewa iyayensu da kowa nasu domin ganin sun biyewa son ransu na auren wadanda zuciyoyinsu suka kwanta musu. A irin wannan yanayin masoyan suka yiwa kawunansu alkawarin zama da juna a kowani irin hali na wuya ko kuwa na dadi.
Masoya masu karancin shekaru suna dauka soyayya kadai ya isa ya zaunar da ma'aurata. A tunaninsu muddin ana son juna to fa babu wanda ya isa ya iya shiga tsakanin su. Wannan yasa suke bijirewa duk wani shawaran da za a basu na rashin dacewar lokaci ko junansu, amma sam ba a kunnensu.
Daga karshe idan sunyi aure tafiya yayi tafiya an soma haihuwa daga wannnan lokacin ake soma fahimtar maganan manya. Wasu idan anyi sa'a auren ya dore cikin wuya da dadi, wasu kuwa cikin wuya wanda wannan wuyan shine yake shafar rayuwarsu su dawo marasa wani buri a rayuwa sai maula da kaskantar da kawunansu.
Tabbas soyayya shine abu na farko da ake dubawa tsakanin masoya kamin a tabbatar da aurensu, amma soyayya ba shi bane ginshiki na zaman auren ba.
Duk yadda masoya suke son junansu muddin shi namijin bashi da abunyi a rayuwarsa, wannan soyayar ba zai taba yin tasiri ba. Haka nan idan akwai soyayya, akwai abun yi amma babu hakuri a tsakanin ma'auratan auren bazai yi inganci ba.
Abunyi ga namiji shine abunda yake baiwa duk wani magidanci damar juya gidansa. Shi yake sa uba ya juya 'ya'yansa ya kuma sauke hakkinsa na uba.
Abun yi ke baiwa maigida damar yin Jima'i cikin natsuwa da iyalinsa. Don haka kamin ka nemi soyayyar wata 'ya ko 'yar wacece, ka tabbatar da cewa kana da abunda kake yi na aiki ko na sana'a ko kuma kasuwanci.
Duk wata macen da ta ce maka zata iya rayuwa da kai cikin kunci da talauci saboda matukar soyayyar da ta ke yi maka, duk zancene na yarinta da rashin sanin yadda rayuwar aure abun take.
Da fatan mata za'a Kula kuma za'a yi tunani sosai wajen abokin rayuwa, Kada son namiji ya rufe miki ido kizo kiyi nadama daga bisani. Ku kuma samari a daure a nemi sana'a domin rayuwar aure sai da sana'a, duk irin yadda kuka kai da soyayya Idan babu sana'a zaman baya yuwa.