Ana yawan ganin miskilai a matsayin mutane masu girman kai ko raini da wulakanci saboda shiru-shirunsu, sai dai kuma ba haka abin yake ba, dabi’arsu ce haka.
Sai dai kuma duk da haka, mata da yawa sun fi son maza masu wannan dabi’ar ta miskilanci fiye da mutum mai haba-haba.
Shafin Bin-Affan ta kawo dalilan da ke sa mace ta so miskilin namiji kamar haka:
1. Suna da kokarin saurarar mutane saboda ba su damu da sha’anin mutane ba.
Samun isasshen lokacin magana da mutane saboda ba su da yawan magana da mutane daban-daban. Sun iya kwantar da hankalin yarinya saboda shirun su yana basu damar su lakanci halayyar mutane.
2. Suna da saurin fahimtar zancen mutane saboda ba kowace magana suke maida hankali a kai ba. Ba su da saurin mita ko korafi saboda shiru-shirunsu.
3. Ba su da nuna takama da alfahari da suke da shi saboda su ba su ga dalilin yin hakan ba. Sukan koya wa mace yadda za ta kula da kanta saboda lokacin da suke da shi na nazartar halayyarta.
4. Suna daga saukin rayuwa, domin su mutanene da ba su daukar rayuwa da zafi komai nasu suna yi ne gwargwadon iyawarsu.
5. Yawancin miskilai za ka same su masu Ilimi ne, Shiyasa duk abinda za su yi suna yi ne cikin Ilimi da basira.
Wadannan sun dalilai biyar da yasa mata da dama ke son auren miskilin namiji fiye da mai haba-haba. Da fatan mun amfana daga abubuwan da muka Karanta.