Wata tattaunawa da mukai da 'yan mata sun bayyana mana abubuwa daban-daban har guda 10 da ke birge su ga maza har su ji sun kamu da Kaunarsu.
Waddannan abubuwan in ji matan, suna cikin wadanda suke fara kalla har su kai ga jan hankalinsu su amince su fara soyayya da namiji.
Sai dai kamar yadda kowa ke da dabi’u da halayen da suka bambanta shi da wani, to haka yake a gurin ’yan mata ma, kowace akwai abin da take kula da shi a gurin namiji, da zai sa ta so shi.
A tattaunawa da mukai da wasu mata kan abin da namiji zai yi ya burge su har su yi soyaya da shi.
Wata budurwa mai suna Nusaiba, ta bayyana cewa, “Ni yadda namiji ke tafiya ne abin da ya fi burge ni da shi.”
Ita kuwa wata mai suna Nafisa Bello cewa ta yi, “Yanayin kwalliya da tsarin namiji da kuma yanayin hankalinsa ne suka fi burge ni. Idan namiji na tunani kamar yaro karami duk kwalliyar shi, zan iya barin shi.”
Sai dai ita kuwa wata budurwar mai suna Goodness Auta, ta ce, “Nauyin aljuhun namiji ne zai sa ni son shi, da kuma tsayi da kyawun shi.”
Ga karin wasu abubuwan da matan suka ce sun fi burge su da maza:
1. Tsawo, mata sun bayyana cewa namiji dogo yana birgesu sosai, hakan yasa su ji suna son sa.
2. Kyan fuska, mata suna son namiji mai kyaun fuska wanda ko aure suka yi suna sa ran za su haifi yara masu kyau.
3.Kwalliya da sa kaya, kowace mace idan ka tambayeta irinsu namijin da tafi so sai kaji ta ce mai kwalliya da tsafta. Mata Sun a son namiji dan gayu sosai.
4. Natsuwa, mata suna son nitsatsen namiji.
5. Kyau, kyan Kira kamar mai gemu da saje mai doguwar fuska da sauransu.
6. Launin fata, kaso 70 cikin 100 na matan da muka tattauna dasu sun bayyana sun fi son farin namiji.
7. Diri/Kira, wasu daga cikin matan sun ce suna son namiji mai diri da Kira.
8. Hankali, mata suna son namiji mai hankali da tunani wanda duk abinda zai yi yana yinsa cikin hankali da tunani.
9. Yanayin kamshin turare, da yawa daga cikin mata sun ce suna son namiji mai kamshin turare hakan ke sa su ji suna kara son sa.
10. Kafa, da yawan mata sun center haduwar farko suna fara duban kafar namiji ne kafin ma su a mince da son sa.
A karshe, ‘yan mata da dama sun bayyana cewa kyau namiji suke kula da a farko.
Da fatan samari za'a koyi darasi daga abubuwan da kuka Karanta na abubuwan da mata suka fi so daga wajen ku.