Mace Balaga Uku 3 Take Yi A Rayuwarta - Android Pols
Idan Takai Mataki Na Uku Batayi Aure Ba Sai Addu'a. Amma Wasu Matan Su Suke zubar da Damar Su a lokacin Balagar Su Ta Farko.
1- Balagar farko yakan fara mata daga 13-19 a wannan lokacin duk wani ɗa namiji idan ya ganta sai ya ƙyasa da burin inama ta zamo matar shi.
Za ta yi farin jini sosai. Zaka ga maza da yawa sun kosa da neman aurenta amma ita a wannan lokacin sai ruÉ—in duniya da rawar ido ya hanata aure.
Wasu kuma iyayenta ne sai suce sai yayyinta sun yi aure. Wanda yin haka zaisa har takai mataki na biyu.
2- A mataki na biyu ne wanda take cikin jerin shekaru 20-25 daga wannan lokacin zaka ga masu neman aurenta sun fara ja da baya.
Ita kanta za ta fara kasancewa cikin tunani wanda a ƙarshe zai iya haifar mata da ciwon zuciya.
Wata kuma wai alkawarin wanine akan ta wanda shine ya sanya ta jinkirin aure amma a ƙarshe sai kaga yaci amanarta ya aure wata daban ba ita ba.
Wanda wata za ta iya rasa ranta akan tunanin wannan abun. Wata kuma Zata ga kamar baƙin jini ta yi amma ba haka bane duk da cewa munsan komai lokacine.
Wannan tunanin zai kai ta ga matakin balaga na uku.
3- Mataki na ƙarshe daga 25-30 babu mai sha'awar aurenta saboda anayi mata ganin kamar ba budurwa bace.
A wannan matakin ne zata kasance babu mai neman aurenta kowa zai yi mata ganin kamar bata damu da yin aure ba.
Duk masu neman ta zasu nisance ta. Zata shiga cikin wani hali wanda ubangijine kawai zai iya kare mata martabar ta.
ƙannen ta duk sunyi aure. Wasu ma har sun hayayyafa.
Ya Allah ka aurar mana da mataye a lokacin da aure yake son su.
Allah ka aurar dasu suna masu cike da budurcin Su.
Leave Comments
Post a Comment