Kotu ta umarci a yanka wani Zakara a Kano Saboda Yana Hana Makocinsa Barci - Android Pols


Kotun Majistiri da ke gidan Murtala a Kano ta umarci wani mutum Isyaku Shu'aibu da ke unguwar Ja'en ya yanka Zakaransa.


Freedom Radio ta rawaito cewa Maƙocinsa Malam Yusuf Muhammad Ja'en ne ya shigar da ƙara Kotun kan cewa Zakaran yana shiga haƙƙinsa ta hanyar hana shi barci da yawan Cara.


Amma ko da aka karantowa wanda ake ƙara ya ce, gaskiya ne Zakaran na yawan yin Cara kuma zai yanka shi ne a bikin "Good Friday" don haka ya roƙi Kotun da ta sahale masa zuwa ranar.


Mai shari'a Halima Wali ta amince inda ta umarci ya killace Zakaran kuma ya yanka shi a Juma'a mai zuwa wato ranar "Good Friday" ɗin.


Mutane ne dai da yawa ke ta bayyana ra'ayoyinsu akan wannan batun wanda ana iya cewa bakon abu new domin ba kasafai aka fiya shigar da kara irin wannan ba. Me za ku ce? 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post