Abin lura Nonuwan mata Sun kasu kashi Biyu, akwai mata masu manya nonuwa. Sannan Akwai masu kananan nonuwa, zan yi muku cikakken bayanin su daya bayan daya Insha Allahu.
1. Manyan Nonuwa
Su wadannan nau'in nonuwa su na da matukar daukar hankalin duk wani da damiji,
musamman in ya kasance sabuwar balaga. Irin Wadannan Nau'in nonuwa sukan cika kirjin budurwa a lokacin da ta ke ganiyar kuruciyarta.
Amma yawanci da Zarar mace mai irin wannan manyan nono ta yi aure ta haihu shikenan sai nonuwan su koma su fadi gaba daya kamar an fasa leda. Mata masu irin Wadannan nonuwan ba su cika burge Mazajensu ba.
2. Kananan Nonuwa
Su Kuma wadannan nau'in nonuwa sune suka fi daukar hankalin mazaje, sai dai ba duk da namiji ne da duk ma'abociyar irin Wadannan nonuwa ke daukar hankalin sa ba, Sannan kuma su wadannan kananan nonuwa sun Kasu kashi biyu (2) ne:.
1. Akwai nono Mai kan-tasa, su nau'in wadannan nonuwa sukan tsiro ne daga kirjin budurwa da kaurinsu, Sannan kuma suna da fadi daga tushe, irin wadannan nonuwa ko da yaro ya sha su basa faduwa sai dai su koma su tsaya cak tamkar Sabuwar budurwa.
2. Akwai kuma nau'in nonuwa na biyu sune mafiya kankanta a ikin nonuwa mata, su wadannan nonuwa suna da tsawo kadan amma ba su da kauri.
Kuma idan yaro ya sha su basa faduwa gaba daya, sai dai su dan kwanto sannan daga samansu su dago kadan. Mata masu irin wadannan nonuwa na burge mazajensu sosai.
Sai dai anan ku sani cewa ko wane irin kalar nono ne dake yana iya zubewa idan ba'a kulawa dashi yadda ya kamata, amma idan ana bin hanyar kula dashi duk girmansa ba zai Kwanta ba.
Ga kadan daga cikin dalilan da suke jawo nono saurin zubewa kamar haka:
1. Saka damammiyar riga babu breziya.
2. Kwanciya ruff da ciki.
3. Kwanciya da breziya.
4. Daurin-Kirji da zani ko towel.
5.Yawan daukar kaya masu nauyi.
6.Yawan yawo a cikin rana mai tsananin zafi.
7.Yanayin halittar mace.
8.Karancin-Sinadarin da ke hana nono saurin zubewa.
9.Halin ko in kula da wasu matan kan yiwa nonuwansu.
Karin-Bayani:. Yana da kyau 'Yan uwana mata ku Sa ni cewa kowacce mace akwai yanayin halittar nononta, sannan wani lokacin nono yana da alaka da yanayin halittar jikin-mace, da kuma yanayin abincin da ta ke ci.
Idan mace ta kasance tana yawan cin abinci mai gina jiki, sannan tana shan abubuwan da suke karawa nono kyau da girma, kuma tana kiyaye duk abubuwan da kan saka nono lalacewa dole ne kiga nononta a tsaye ko da yaushe.
Sabanin Wacce Bata Samun Damar Yin hakan. Saboda haka kowace mace tana cikin matan da yanayin halittar su ne na rashin girman nono da tsayawarsa idan har tana iya kokarinta wajen kula da su to lallai da wuya kiga nononta sun lalace da wuri saboda irin kokarin da ta ke yi A kansu.