Irin Hiran Da Za Ka Dauke Hankalin Budurwa Dasu - Android Pols



A ci gaba da kawowa samari ko nace maza wasu dabarun shawo kan mata. A wannan darasin zai koyawa mazan yadda za su shawo kan mace ta hanyar janta da hira.


Duk yadda kake son mace muddin ba za ta baka lokaci ba bazaka samu shawo kanta ba. Su kuma mata sai da dabaru ake iya samun hankalinsu harma su saurari mutum.


Ga wasu hiran da nan take zaka iya jawo hankalin mace dasu kamar haka:


1. Idan kana son jan hankalin mace ta hanyar jan ta da hira, zo mata da hiran abubuwan da suke faruwa a daidai wannan lokacin. Labarin da ya mamaye gari ko kasa da kowa yake yi.


Idan ka fahimci tasan labari nemi ta sanar dakai abunda yake faruwa. Idan kuma ka fita sani lambarta mata.


Mata suna son jin labari, wannan yasa za ta so jin labarin ga wanda yake da masaniya.


Kada ka sako mata da zancen soyayya a wannan lokacin. Amma dai ka nuna mata saboda matsayinta a wurinka yasa kake wannan hiran da ita.


2. Kai tsaye nuna mata ta burgeka akan natsuwanta, kwalliyarta da dabi'unta.


Kace mata wannan ne ma yasa kake ta zumudin ku gaisa. 


Dauki lokaci mai tsawo kana yi mata bayanin abubuwan da suka burgeka game da ita. 


Mata suna son a yabesu. Hakan yasa suke sauraron duk wanda zai nuna musu kaunarsa garesu koda ba ta soyaya bane.


3. Idan 'yar Boko ce zo mata da hiran boko da karfafamata akan karatu da kuma nuna mata irin matan da kake so kenan. Haka nan idan Islamiya take yi ka yi mata zancen tare da yi mata fatan alheri.


Mata suna son duk wanda zai karfafa musu gwiwa akan abunda suke burin zama a rayuwa. Wannan yasa za ta baka kulawa tare da tuntubarka akan neman shawara neman fahimtar wani abu da ta kasa fahimta na karatu.


4. Idan kana son jan hankalin mace ta hanyar hira da ita. Ka kirkiro hiran da zai sa ku yin musu da juna. Ka musanta wani abinda ta fika gaskiya akai, koda wani za'a tambaya shima ita zai goyawa baya.


Wannan musanta abunda ta san gaskiyansa da za ka yi, zata nemi ta dage sai ta gamsar da kai saboda tasan tana da hujja.


Mace muddin tasan tana kan gaskiyaryarta, ba za ta taba hakura da hiran ba har sai wanda take musun da shi ya gamsu.


5. Idan za ka zowa da mace da hiran yadda za ta inganta rayuwarta domin cimma burinta. Za ta ajiye komai da take yi domin sauraranka.


Mace duk lalacewarta, tana son taji ana bata shawarwarin da za su amfaneta koda kuwa ba aiki dasu za ta yi ba.

 

Ba duk mata bane suke son namiji yace musu yana sonsu kai tsaye ba, ba tare da ta fahimci akwai abinda yasa ka furta mata kalmar so ba.


Mace tana iya ganin gilmawar mutum kawai taji ta kamu da sonsa. Amma shi namiji yana kamuwa da son mace ce saboda wasu abubuwan da ya gani tare da ita. Wannan yasa idan kacewa mace kana matukar sonta a haduwarku na farko bazata yarda ba.


Da fatan samari za'a yi amfani da wadannan dabarun domin sace zuciyar wacce kake so. Amma Idan har kasan ba da aure za kaje wajenta ba Kada ka yi hakan. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post