Mata sunada wasu dabi'u da halayen da suke yiwa namijin da basa son shi.
Gasu halayen da dabi'un da zaran ka fahimci mace na yi maka su, babu soyayyarka a zuciyarta.
1: Bazata taba yarda ta baka lambarta ba da hannunta. Kana tambayarta lambarta zata ki baka kai tsaye, ko kuma tace maka batada waya.
Muddin mace ta hanaka lambarta batada sha'awar yin soyayya dakai ne.
2: Bazata yarda ka zo gidansu. Mace idan bata sonka duk yadda zaka yi bazata yarda ta amince kazo wajenta a gidansu ba.
Don haka muddin ka nemi zuwa gidan wacce ka gani kana so tace maka kada kazo ko ba yanzu ba. Ka saka a ranka kawai bata sonka ne.
3: Mace idan bata sonka, kana mata magana zata kiraka da Baba na, ko Ankul ko kuma yaya na. Kana jin tace haka ka hakura kawai baka samu shiga ba.
4: Idan mace bata ra'ayinka kana nuna mata kana sonta zata turo maka wata kawarta ko kanwanta nace na maka mata.
Haka matan da basa son namiji suke yi masa kora da hali.
5: Duk irin talaucin mace idan batason namiji bazata barshi ya saya mata wani abu idan sun hadu a kanti ba, ko ya biya mata wani abunda ta saya da kanta.
Mace idan bata sonka tana gudun cin abun hannunka. Idan kuma tana sonka abun hannun naka bai dameta ba.
6: Muddin kaji mace na maganar saurayinta ko samarinta a gabanka, idan baka furta mata kalmar soyayya kawai kayi shuru. Tana bada wannan labarin ne saboda ta tokareka ganin alamun kana sonta ko ka riga da kayi mata zancen soyayya.
Mace idan tana sonka kokarin boye maka halin da take ciki na soyayyar tane amma ba ta fito fili ta yayata maka ba.
7: Idan mace bata sonka ba duk wayan da ka kirata zata dauka ba. Haka nan ba duk sakonka na text bane zata maka replay ba.
Haka nan kuma bazata taba baka hakuri ko uzurin rashin yin abunda tayi ba.
8: Ita mace idan bata sonka nesa take da kai bama taso ka kusanceta bare ma kuskure yasa jikinta ya taba naka.
9: Mace idan bata sonka batada lokacinka. Idan za a shekara kana neman ta baka lokaci kazo ka ganta zata rika baka uzurin da kanka zaka hakura.
10: Idan mace bata sonka bazata taba girmamaka ba. Musamman idan ka nace mata da sai ta baka hadin kai.
Sai dai kuma a wani lokacin mata suna son naci. Idan zaka iya nace mata idan har da rabonka zata iya sauya ra'ayi.
Abin lura anan shine ba dole wannan dalilin da muka ambata ya tabbatar ba ta sonka ba.