Hakika matsalar Istimna'i, zinar hannu (wato Masturbation) da hausa kuma (ko kuma duk wata hanya ta fitar da maniyyi bata jima'i ba, kuma ba a mafarki ba ) gagarumar matsala ce wacce take shiga zuciyar masu yinta, tayi kaka-gida.
Kuma tana da wahalar fita gaba dayanta dole sai dai albarkacin addu'a da kuma yawaita ibada mutum zai samu wadatuwar tsoron Allah a zuciyarsa harma ya zamto ba zai iya aikatawa ba.
Na tattauna da mutane masu yawa a wannan satin a kan lamarin inda yawanci suna kukan yaya za su yi su rabu da wannan matsalar sudaina yi, suna cewa koda sun daina suna kara komawa basa'iya bari, Wasu daga cikinsu suna cewa gaba daya basa iya haddace karatu wanda dalilin matsalar aikata Istimna'i ta kawo musu hakan.
Wasu Kuma suna cewa haka kawai suke zubarda maziyyi koda wa'azi sukaji anayi akan mace, wasu kuma na cewa kankantar gabane yake damunsu, Wasu Kuma Ya haifar musu da matsalar ido, Wasu Kuma tsananin ciwon baya, Dan Allah ai Ya kamata kodan wannan mutum ya tuba yabar aikata wannan abin.
Mafiya yawan samari suna yi ne bisa niyyar wai zasu kauce ma yin ZINA. Basu san cewa shima wannan din babban Kaba'ira bane, kusan babu wani bambanci.
Matasa Maza da Mata da dama sun afka cikin wannan bala'in. Wasu cikin rashin sanin illolinsa, wasu kuma saboda tsabar Fajirci.
Kuma kamar yadda zina take da mutukar Illa tana cutar da lafiyar mutum, ta chutar da hankalinsa, da gurbata tunaninsa, ta cire masa Kwayar Imani da tsoron Allah daga zuciyarsa. Hakan shima Istimna'i yake lalata rayuwar mutum da mutuncinsa da lafiyarsa.
Lallai wajibi ne ga duk mutumin da yake son kansa da arziki, kuma yake fatan gamuwa da Allah lafiya, ya nisanci Zina da dangoginta irin su Luwadi, Madigo, Istimna'i, da sauransu.
Kamar yadda ake ta fada anan a kafafen Wa'azantarwa da fadakarwa . Babbar hanyar da zaka bi/zaki bi domin rabuwa da wannan bala'in na yin wasa da al'aura don biyawa kai bukata sun hada da :
1 Yin aure
2 Yawaita azumi
3 Nisantar duk wani hoto ko
Video mai nuna tsaraici. (Ka gogeshi daga wayarka)
4 Nisantar shafukan Internet
masu nuna tsaraici.
5 Daina abota da fitsararrun abokai / kawaye.
6 Nisantar duk wajen da ake cudanya tsakanin maza da mata.
7 Ka daina zama kai kadai a cikin daki in dai ba ibada kake yi ba.
8 Yawaita karatun Alqur'ani da zikirin Allah.
da sauran ayyukan alkhairi.
9 Zama cikin Mutanen kirki, karanta labaran mutanen kirki tare da kokarin koyi dasu.
10 Tuna Allah a ko yaushe da kuma tunowa kusancinsa gareka a duk inda kake.
11 Tuna kusancin ajalinka, fitar ranka, kwanciyar Qabarinka, hisabinka, da kuma masaukinka na karshe. Wuta ko Aljannah.
12 Fita daga duk wani Group ko shafi na
batsa a Facebook ko Whatsapp wanda
suke kunshe da abubuwan batsa, tare da nisantar abokai masu tura abubuwa da ya danganci batsa.